An Samu Sababbin Bayanai game da 'Tashin Bam' a Asibitin Kebbi

An Samu Sababbin Bayanai game da 'Tashin Bam' a Asibitin Kebbi

  • Gwamnatin Kebbi ta karyata jita-jitar fashewar bam a babban asibitin Bagudo inda ake zargin jama'a sun shiga mawuyacin hali
  • A karin haske da gwamnatin Jihar ta fitar, ta bayyana cewa ba bam ne ko wani harin 'yan ta'adda aka kai babban asibitin ba
  • Gwamnatin ta kara da cewa an dauki matakan da suka dace wajen killace wurin da dakile yaduwar tashin hankali a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi karin haske game da abin da ya faru a babban asibitin Bagudo da ke karamar hukumar Bagudo, a safiyar Talata, 30 ga Disamba, 2025.

Gwamnatin ta bayyana cewa ƙarar fashewar da ta razana jama’a ba fashewar bam ba ce, illa dai gobarar wuta ce da ta tashi a cikin wurin ma’aikatan asibitin.

Kara karanta wannan

Mutane sun ga tashin hankali bayan abin fashewa ya tashi a asibitin Kebbi

Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da fashewar abu a wani asibiti
Gwamna Nasir Idris kauran Gandu Hoto: Yahaya Sarki
Source: Facebook

Wannan karin bayani ya fito ne daga bakin Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida wanda hadimin Gwamna kan yada labarai, Yahaya Sarki ya wallafa a shafin Facebook.

An yi bincike 'fashewar bam' a Kebbi

Sanarwar ta ce sakamakon binciken farko da rahotannin hukumomin tsaro suka bayar sun nuna cewa gobara ce ta haddasa ƙarar, ba wani abu mai fashewa ba kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Ya jaddada cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta ba su da tushe ballantana makama na cewa abin fashewa ne ya tarwatse a asibitin.

Alhaji Yakubu Bala Tafida ya ce gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro, wadanda tuni suka karɓi ragamar aikin.

Ya tabbatar wa al’umma cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar, duk da cewa wani gini ya lalacewa. Ya ƙara da cewa mutanen da ke cikin ginin sun samu damar ficewa lafiya kafin gobarar ta tsananta.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

Ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa yada bayanan da ba a tantance ba, waɗanda ka iya haddasa firgici da tashin hankali a cikin al’umma.

Gwamnatin Kebbi na samar da tsaro

Sakataren Gwamnatin ya bayyana cewa dukkanin hukumomin tsaro, ciki har da ‘yan Sanda, Sojoji da sauran sassan tsaro, suna kan lamarin domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Ya ce ana ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin tashin gobarar, domin daukar matakan da suka dace a nan gaba.

Gwamnati ta ce ba bam ne ya tashi a Kebbi ba
Taswirar jihar Kebbi, inda abu ya fashe a asibiti Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnatin Jihar Kebbi ta yabawa rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi da sauran jami’an tsaro bisa saurin daukar mataki da suka yi, inda suka killace yankin cikin gaggawa tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wannan mataki ya taimaka matuka wajen hana yaduwar firgici da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin, sannan gwamnati ta kara da bayar da tabbacin tsaron rayukan jama'a a Kebbi.

Ta tabbatar wa mazauna jihar cewa tsaro da lafiyarsu na daga cikin manyan abubuwan da take ba muhimmanci, kuma ana daukar dukkannin matakan da suka dace domin kaucewa sake afkuwar hakan.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Wani abu ya fashe a Kebbi

A wani labarin, mun wallafa cewa hankula sun tashi a jihar Kebbi bayan wani abin fashewa ya auku a asibitin gwamnati na Bagudo da ke ƙaramar hukumar Bagudo, lamarin da ya jawo fargaba.

Lamarin ya faru ne da sassafe a ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025, inda ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali ba tare da an samu tabbacin abin da ya afku ba.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarar fashewar ta razana mazauna yankin, lamarin da ya sa jama’a suka rika zargin yiwuwar kai hari. Ita ma rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta fito ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng