Peter Obi: An Ji Yadda Gwamna Mai Ci Ya Tube, Ya Wanke Bandaki Mai Kazanta a Jirgin Sama

Peter Obi: An Ji Yadda Gwamna Mai Ci Ya Tube, Ya Wanke Bandaki Mai Kazanta a Jirgin Sama

  • Peter Obi ya ba da labarin yadda ya wanke wani bandakin jirgin sama lokacin yana ofis a matsayin gwamnan jihar Anambra
  • Obi, wanda ya yi takarar shugaban kasa a inuwar LP a zaben 2023, ya amsa tambayoyi kan yadda zai magance matsalar tsaron Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya ce samar da kyakkyawan jagoranci na da matukar muhimmanci wajen fuskantar duk wani kalubale da ya addabi jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - Dan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, ya ce jagoranci nagari kuma abin misali na da matuƙar muhimmanci wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.

Tsohon gwamnan ya kuma ba da labarin yadda ya cire girman kai, ya wanke bandakin jirgin sama mai cike da kazanta duk da a lokacin yana matsayin gwamnan Anambra.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Peter Obi ya yi karatun ta natsu, ya gano wanda ya dace ya mulki Najeriya

Peter Obi.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Mista Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

Peter Obi ya kawo mafita kan tsaro

Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga ’yan Najeriya a wani taron tattaunawa na X Space a ranar Lahadi.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce harkar tsaro ta tabarbare sosai, kuma hakan na buƙatar shugabanni masu nuna ladabi, ɗaukar alhaki da kwatanta gaskiya a aikace.

Yayin da yake amsa tambaya kan yadda zai tunkari matsalolin tsaro, Peter Obi ya ba da labarin wani abin da ya faru da shi domin bayyana irin salon jagorancin da yake da shi.

Ya ce a lokacin da yake gwamna, ya taɓa tafiya a jirgin sama na kamfanin British Airways, inda ya tarar da bandakin cikin jirgin cikin mummunan yanayi na kazanta.

Yadda gwamna ya wanke bandakin jirgi

A cewarsa, wata mata da ke aiki da gwamnatin Jihar Lagos a ƙarƙashin tsohon gwamna Babatunde Fashola ta buɗe bandakin, ta ga yadda yake, sannan ta rufe ta tafi.

Kara karanta wannan

'Makaman da Amurka ta harbo Najeriya sun kara tona asirin Gwamnatin Bola Tinubu'

Obi, wanda a wancan lokacin gwamna ne, ya ce shi ya shiga bandakin ya tsaftace shi da kansa ba tare da sanar da kowa ba.

“Akwai wata mata da ke aiki da gwamnatin Jihar Lagos a lokacin Fashola, tana aiki da wata tawagar lauyoyi.
“Muna dawowa ne a jirgin British Airways a wancan lokacin, ni kuma ina kan mulki a matsayin gwamna. Bandakin jirgin ya lalace ƙwarai. Ta buɗe shi da nufin ta biya bukata ta ga yadda yake, sai ta tafi.
“Ni kuma na shiga ciki na tsaftace shi. Daga baya ta dawo ta tarar da komai ya gyaru. Ba ta faɗa min komai ba, sai dai ta faɗa wa wani minista da wasu a ofishinta."

- In ji Peter Obi.

Peter Obi.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi ya ja hankalin 'yan Najeriya

Bisa haka, jagoran LP ya bukaci mutane da su rika daukar alhakin gyara abin da suka gani ba daidai ba, matukar suka samu ikon hakan, kamar yadda The Cable ta rahoto.

“Idan ka ga wani abu ba daidai ba, ka gyara shi. Ban da masu aikin gida a gidana; kowa ya san hakan. Mu daina rayuwar ƙarya," in ji shi.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Obi ya gama shirin komawa ADC

A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, ya kammala shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a hukumance.

Wata majiya ta bayyana cewa za a gudanar da gangamin bayyana matsayarsa a birnin Enugu, cibiyar siyasar yankin Kudu-maso-Gabas, a ranar 31 ga Disamban 2025.

A cewar majiyar, magoya baya da mabiyan Peter Obi sun riga sun fara shirye-shiryen sauya shekar domim marawa maigidansu baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262