Mutane Sun Ga Tashin Hankali bayan Abin Fashewa Ya Tashi a Asibitin Kebbi

Mutane Sun Ga Tashin Hankali bayan Abin Fashewa Ya Tashi a Asibitin Kebbi

  • Hankulan mutane sun tashi bayan wani abin fashewa ya tashi da sassafe a wani asibitin gwamnati da ke jihar Kebbi
  • Lamarin wanda ya jefa mutane cikin firgici da tashin hankali ya auku ne da safiyar ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025
  • Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana matakan da ta dauka domin shawo kan matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Hankula sun tashi bayan wani abun fashewa ya tashi a asibitin gwamnati na jihar Kebbi.

Fashewar ta auku ne a ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025 a asibitin gwamnati na Bagudo, a jihar Kebbi.

Abin fashewa ya tashi a asibitin jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Punch ta ce rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Rundunar 'yan sandan ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ba sakamakon fashewar da ta auku.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

Rahotanni sun nuna cewa fashewar ta auku ne da sassafe a ranar Talata, lamarin da ya haddasa firgici da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun dauki mataki cikin gaggawa tare da killace yankin domin kauce wa barazana ta gaba.

"Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi na tabbatar wa jama’a cewa muna da cikakken iko kan tsaro bayan fashewar da ta auku a asibitin gwamnati na Bagudo.”

- SP Bashir Usman

Ya bayyana cewa tawagar hadin gwiwa ta tsaro da ta kunshi ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai sun kewaye yankin nan take, yayin da aka tura kwararrun jami’an EOD–CBRN (masu kula da abubuwan fashewa da sinadarai masu hadari) domin bincikar wurin.

“Mun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa. Duk da cewa wani gini a cikin mazaunin ma’aikata ya lalace, amma mazaunansa sun riga sun fice cikin tsaro."

- SP Bashir Usman

Za a kara tura jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta soki gwamna da ya yi gum da bakinsa bayan harin Amurka a jiharsa

A cewarsa, kwamishinan ’yan sandan jihar ya bayar da umarnin kara tura jami’an tsaro na musamman zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kwantar da hankulan jama’a.

'Yan sanda sun fara bincike kan tashin bam a Kebbi
Jami'an rundunar 'yan sanda a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter
"Bincike mai zurfi na gudana domin gano musabbabin fashewar, kuma za mu sanar da jama’a duk wani karin bayani idan ya taso.”

- SP Bashir Usman

Rundunar ’yan sandan ta bukaci al’umma da su kwantar da hankulansu, tare da kauce wa kusantar yankin asibitin a halin yanzu, domin ba jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata yayin da ake ci gaba da bincike.

Bam ya tashi a Maiduguri

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu fashewar bam a wani masallaci da ke birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wani dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din da misalin karfe 6:00 na yammaci a wani masallacin Gamboru a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Majiyoyi sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu bayan dan kunar bakin waken ya tayar da bam a masallacin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng