Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari a Kebbi
- An shiga jimami a jihar Kebbi bayan 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani kazamin hari a karamar hukumar Shanga
- Harin na 'yan bindiga ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama tare da jikkata wasu daban da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa ta tura jami'an tsaro zuwa yankin da aka kai hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - ’Yan bindiga sun kai wani mummunan hari kan al’ummar kauyen Gebbe da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi.
Mummunan harin na 'yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu da yawa suka jikkata.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya
Mutanen da suka tsira da rayukansu sun rika tserewa cikin firgici zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su dazuzzukan da ke kusa da yankin.
'Yan bindiga sun kai hari a Kebbi
Majiyoyin sun ce maharan sun afkawa al’ummar kauyen ne ba tare da wani gargadi ba, suna harbe-harbe ba kakkautawa, abin da ya haddasa tsoro da rikice-rikice a tsakanin jama’a.
An bayyana harin a matsayin mafi muni da yankin ya fuskanta cikin shekaru masu yawa, inda hakan ya tilasta wa mazauna kauyen barin gidajensu domin neman mafaka, tashar Channels tv ta dauko labarin.
"Jama'a sun shiga tashin hankali matuka. Ba mu taba fuskantar irin wannan ta’asa ba tsawon lokaci."
- Wani mazaunin yankin
Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba, kasancewar jama’a sun watse zuwa bangarori daban-daban yayin harin, lamarin da ya sa ya yi wahala a gano girman barnar nan take.
Me 'yan sanda suka ce kan harin?
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce harin ya faru kuma an tura jami’an tsaro zuwa yankin.
Ya bayyana cewa ’yan sanda na ci gaba da tantance halin da ake ciki domin gano adadin wadanda suka mutu da kuma irin raunukan da aka samu, yana mai cewa za a fitar da cikakkiyar sanarwa daga baya.
“An sanar da mu game da harin, kuma an tura tawagar jami'an tsaro zuwa yankin domin samun sahihin bayanai kan abin da ya faru da kuma adadin wadanda abin ya shafa." -
SP Bashir Usman

Source: Original
An tura jami'an tsaro
Wasu mazauna yankin, da suka nemi a boye sunayensu, sun tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun fara shiga yankin domin dawo da kwanciyar hankali.
A halin da ake ciki, mazauna yankin da ke cikin damuwa sun yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa, suna bayyana harin a matsayin mummuna.
Yunkurin jin ta bakin dagacin kauyen bai yi nasara ba, domin bai dauki kiran wayar da aka yi masa ba.
'Yan bindiga sun kai hari a Gombe
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Pindiga da ke jihar Gombe.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara bayan gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Kano
'Yan bindigan sun kashe wasu 'yan gida daya su biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane huɗu a harin da suka kai a kauyen da ke karamar hukumar Akko.
Lamarin ya jefa al'ummar yankin cikin babban tsoro da fargaba, musamman ganin yadda maharan suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Asali: Legit.ng
