Magana Ta Fito: Wike Ya Fadi Dalilin Rikicinsa da Gwamna Makinde

Magana Ta Fito: Wike Ya Fadi Dalilin Rikicinsa da Gwamna Makinde

  • Alaka ta yi tsami tsakanin Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde
  • A kwanakin baya, Gwamna. Seyi Makinde ya fito ya yi zarge-zarge kan Wike wanda a baya ya kasance makusancinsa
  • Sai dai, Wike ya fito ya bayyana dalilin da ya sanya ake rikici tsakaninsa da gwamnan Oyo duk da sun kasance 'ya'yan jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa tushen takaddamar da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Wike ya bayyana cewa rikicin su ya samo asali ne bayan Gwamna Seyi Makinde bai samu gurbin kawo Minista a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

Wike ya yi magana kan rikicinsa da Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @seyimakinde, @GovWike
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Wike ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Wike ya yi bayani kan dalilan da suka haifar da tabarbarewar alakarsu da kuma matsalolin siyasa da ke kunshe a cikin kungiyar G5.

Me ya hada Wike da Gwamna Makinde?

A cewar Wike, matsalar ta fara ne lokacin da Makinde ya kasa samun mukamin minista ga mutumin da ya tsayar, duk da yarjejeniyar da aka yi a baya a cikin kungiyar.

“Abin da muke fuskanta a yau shi ne matsalar da ta taso saboda bai samu ko da mukamin minista daya ba."
“Ko a lokacin da yake magana, fushi yana bayyane a fuskarsa. Bai ma bukaci ya fada ba, mun gani da idonmu. Mun ce masa, ‘ka kwantar da hankalinka."

- Nyesom Wike

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce an yi kokari sosai wajen lallashin Makinde tare da masa bayani kan dalilan da suka shafi nadin mukaman, har da kai ziyara ga Shugaba Tinubu, tashar Channels TV ta dauko labarin.

“Mun koma gida muka yi masa bayanin dalilin da ya sa muka je ganin shugaban kasa. Mun ce masa ya dan yi hakuri. Akwai wasu abubuwa da watakila bai yi la’akari da su ba. Amma dai dole ne a yi wani abu."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba na shirin barin NNPP, Wike ya aika sakon gargadi ga masu shiga APC

- Nyesom Wike

Wike ya yi wa Gwamna Makinde martani
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Makinde ya ki yarda da yunkurin sulhu

Ya kara da cewa duk da kokarin da aka yi, Makinde ya nuna kamar tuni ya yanke shawara, lamarin da ya sanya sulhu ya gagara.

Babban Ministan harkokin na Abuja ya kwatanta martanin Makinde da na mutumin da ya samu nasara da wuri, wanda hakan ya sanya ya zama mai gajen hakuri.

“Wani lokaci idan ka samu dala miliyan 1 a karon farko, sai ka yi gaggawar daukar mataki. Ka manta cewa Dangote ba shi ne ya fi kowa gaggawar samun dala miliyan daya ba, amma a yau shi ne mutum mafi arziki a Afirka."

- Nyesom Wike

Nyesom Wike ya yarda ana yawan zaginsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana kalubalen da yake fuskanta a sjyasa.

Nyesom Wike ya bayyana cewa shi ne dan siyasar da ake zagi fiye da kowa a Najeriya a halin yanzu bayan Shugaba Bola Tinubu.

Ministan ya bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da nuna goyon bayansa ga Shugaba Tinubu duk da kalubalen da yake fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng