Jami'an Tsaro Sun Yi Arangama da Mutanen Gari a Katsina, An Rasa Rayuka
- Harsasai da suka fita daga cikin bindigan 'yan sandan Najeriya sun yi ajalin mutane biyu a Katsina, bayan afkuwar wata hatsaniya
- Rikici ya barke tsakanin jami'an tsaro da mutanen gari ne lokacin da aka je kama wani matashi mai suna Kuda a Sabuwar Unguwa
- Rahoton 'yan sanda ya yi bayani dalla dalla kan yadda fusatattu suka kona ofishin NSCDC da kuma yadda mutuwar matasan ta kasance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - An samu tashin hankali a yankin Sabuwar Unguwa da ke jihar Katsina bayan mutanen yankin sun yi arangama da jami'an tsaro.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce wannan hargitsi da aka samu ya jawo mutuwar wasu mutanen gari da raunata jami'an tsaro.

Source: Facebook
Samamen 'yan sanda a jihar Katsina
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sandan jihar, DSP Aliyu Abubakar Sadiq ya fitar, wacce aka wallafa a shafin rundunar na Facebook.
Sanarwar DSP Aliyu ta nuna cewa:
"Rundunar 'yan sandan Katsina na sane da wani mummunan lamari da ya faru a wajen jana'izar wani marigayi Uzairu da aka fi sani da Kuda a Sabuwar Unguwa, Katsina. Wasu bata gari sun shiga cikin masu jana'izar, inda suka tayar da hargitsi."
Rundunar 'yan sanda ta ba da labarin yadda komai ya faru da cewa a ranar 27 ga Disamba, 2025, bisa bayanan sirri, ta kai samame maboyar masu aikata laifi a Sabuwar Unguwa.
Katsina: Kuskuren harbin bindiga ya kashe matashi
Sanarwar ta ce a lokacin da 'yan sanda suka isa wajen, sun kama Uzairu, watau Kuda, bisa zargin safarar kwayoyi ga masu aikata munanan laifuffuka a cikin birnin Katsina.
"An samu Kuda dauke da miyagun kwayoyi da kuma makamai masu hatsari. Kuma ya yi turjiya yayin da ake kokarin kama shi, lamarin da ya jawo hankalin wasu 'yan daba, suka farmaki tawagar 'yan sanda, suka lalata motar rundunar da raunata jami'ai.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara bayan gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Kano
"Wadannan bata garin, a kokarinsu na kwace bindigar wani jami'in dan sanda, suka daba masa wuka, wanda a kokarin kare makamin ne bindigar ta tashi, wanda harsashi ya samu Kuda. Aka garzaya da shi asibiti, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa."
- DSP Aliyu Abubakar Sadiq.
Arangamar 'yan sanda da mutane a Katsina
A washe garin ranar da abin ya faru, watau 28 ga Disambar 2025, rundunar 'yan sanda ta ce wasu fusatattun matasa sun bankawa ofishin hukumar NSCDC wuta da ke Sabuwar Unguwa don huce takaicin mutuwar Kuda.
Sannan, a lokacin da ake shirin birne gawar Kuda, wadannan bata-garin sun kuma yi kokarin kone ofishin 'yan sanda, kamar yadda sanarwar DSP Aliyu ta nuna.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"An yi gaggawar tura karin jami'an 'yan sanda zuwa wurin da ake kokarin kona ofishin. Tare da hadin gwiwar jami'an NSCDC, aka yi kokarin kwantar da tarzomar da ta tashi.
"Sai dai kuma, cikin wani yanayi na bakin ciki, lamarin sai ya munana, inda aka sari wani jami'i da adda, tare da lalata motocin 'yan sanda na sintiri."

Source: Original
Bindigar 'yan sanda ta yi ajalin karin mutum 1
Sanarwar 'yan sandan ta ce al'amura sun dauki wani sabon salo bayan harsashin bindigar da jami'ai suka harba ya samu mutane biyu, wadanda aka garzaya da su asibiti.
"Abin bakin ciki, likitoci sun tabbatar da mutuwar mutum daya daga cikin wadanda aka harba, yayin da dayan yake ci gaba da samun kulawar likitoci.
"Zuwa yanzu dai an kwantar da hankula a yankin. Kwamishinan 'yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano bakin zaren komai."
- DSP Aliyu Abubakar Sadiq.
Rundunar 'yan sandan Katsina ta yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu, su kuma ba hukumar damar gudanar da bincike tare da alkawarin fitar da karin bayani nan gaba.
Karanta sanarwar a nan kasa:
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labari, mun ruwaito cewa, jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar dakile wani mugun nufi da 'yan bindiga suka shirya.
'Yan sandan sun dai samu nasarar ne bayan samun rahoton cewa 'yan bindiga sun tare wasu matafiya da ke kan hanyar Funtua zuwa Gusau.
Bayan an yi artabu tsakanin jami'an tsaron da 'yan bindiga, an samu nasarar kubutar da mutanen da aka yi yunkurin yin garkuwa da su tare da fatattakar miyagun.
Asali: Legit.ng

