Bayan Farmakin Amurka a Sokoto, Mayakan ISWAP Sun kai Kazamin Hari Yobe
- An kai wasu hare-hare da aka danganta ga ISWAP a wasu kauyukan Jihar Yobe, kwanaki kadan bayan Amurka ta kai hari ta sama a Arewa maso Yamma
- Rahotanni sun nuna cewa an jikkata wani basarake a wani kauye, an yi garkuwa da direba, tare da sace kayayyaki daga wata cibiyar lafiya a yankin
- Jami’an tsaro sun kara zafafa sintiri da sa ido, yayin da ake ci gaba da bibiyar motsin ‘yan ta’addan a yankin domin kama su ko dakile barnar su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Yobe – Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin mambobin kungiyar ISWAP ne sun kai mummunan hari kan wasu al’ummomi a Jihar Yobe.
Harin ya faru ne kwanaki biyu bayan rahotannin hare-haren sama da kasar Amurka ta ce ta kai sansanonin mayakan IS a jihar Sokoto.

Source: Original
Kwararren mai bin diddigin harkokin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa hare-haren sun faru da sanyin safiya, inda ‘yan ta’addan suka shiga kauyuka dauke da makamai masu girma.
Yadda 'yan ISWAP suka kai hari Yobe
A cewar majiyoyi, harin ya faru da misalin karfe 12:20 na dare a ranar 27, Disamba, 2025, a kauyen Ja Jibiri. A lokacin harin, shugaban kauyen, Lawan Hassan mai shekaru 45, ya samu rauni bayan an harbe shi a kafadar hagu.
Rahoton ya ce ‘yan ta’addan sun kewaye kauyen cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta mazauna tserewa domin tsira da rayukansu. Bayan harbin shugaban kauyen, maharan sun bar yankin zuwa wani kauye na kusa.
The Guardian ta ce an gaggauta kai Lawan Hassan zuwa Asibitin Geidam domin samun kulawar likitoci, yayin da mazauna kauyen ke nuna fargaba kan yiwuwar sake dawowar maharan.
Mayakan ISWAP sun kai hari Yobe
Daga Ja Jibiri, maharan sun wuce kauyen Ladu, inda suka yi garkuwa da wani direba mai suna Madu Kura, mai shekaru 40, wanda ke tukin wata mota kirar Toyota Hilux.

Source: Facebook
Bugu da kari, ‘yan ta’addan sun kutsa cikin cibiyar lafiya a kauyen, inda suka sace kayayyakin magani da wasu muhimman abubuwa. Haka kuma, sun kwashe wata mota kirar Golf kafin su fice daga yankin.
Matakan tsaro da martanin jami’ai
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun sanar da cewa suna kan shirin ko-ta-kwana, tare da kara yawan sintiri da sa ido a yankunan da abin ya shafa. An ce ana ci gaba da tattara bayanan sirri domin gano inda ‘yan ta’addan suka dosa.
Harin na zuwa ne bayan farmakin ranar 25, Disamba, 2025 da Amurka ta ce ta kai kan mayakan IS a Arewa maso Yamma, inda aka ambaci jihohin Sokoto da Kwara a matsayin wuraren da abin ya shafa.
An kama dan bindiga a jihar Kwara
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wani dan bindiga mai garkuwa da mutane da ake kira da Siddi.
Rahotanni sun nuna cewa dan bindigan da aka kama shi ne mai yawan bidiyo yana nuna wa jama'ar duniya cewa ya tara kudi da makamai.
Dakarun 'yan sanda sun tabbatar da cewa sun kama shi da tsabar kudi har N500,000 da kuma bindiga kirar AK-47 da wasu kayayyaki.
Asali: Legit.ng


