Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara bayan Gwabza Fada da 'Yan Bindiga a Kano
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci cikin dare a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano
- Dakarun sojoji sun yi artabu da tsagerun 'yan bindigan tare da hallaka da dama daga cikinsu bayan gwabza fada
- An samu asarar ran wani dan sa-kai tare da jikkata wani yayin artabun da aka yi da 'yan bindigan a harin da suka kawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - 'Yan bindiga sun ji a jikinsu bayan sun gwabza fada da dakarun sojoji a jihar Kano.
Sojojin sun kashe ’yan bindiga tara a yankunan Bakaji da Unguwar Garma da ke Goron Dutse, a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce shugaban kungiyar tsaron al'umma ta Shanono/Bagwai, Yahya Bagobiri, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, 28 ga watan Disamban 2025.
Sojoji sun gwabza da 'yan bindiga
A yayin arangamar da aka yi da 'yan bindigan, wani dan sa-kai ya rasu, yayin da wani ya jikkata.
’Yan bindigan wadanda suka kutsa yankin a daren ranar Asabar, 27 ga watan Disamban 2025 sun fafata da sojoji a wata musayar wuta da ta dauki tsawon sa’o’i da dama.
Yahya Bagobiri ya ce ’yan bindigan sun tsere ne bayan da sojoji suka yi musu ruwan wuta, inda suka tafi da shanu kusan 40 tare da mutane shida suka sace.
“Sojoji sun kashe ’yan bindigan tare da kwato babura, amma daga bisani tsagerun sun sake dawowa da misalin karfe 5:00 zuwa 6:00 na safe, inda suka bude wa sojoji wuta, sai dai ba su samu damar kutsawa yankin ba."
“Saboda sun zo da yawa sosai, sun sake sace mutane shida tare da kwashe shanu 40. Amma godiya ga sojoji da suka mayar da wuta, inda suka kashe ’yan bindiga tara, lamarin da ya sa sauran suka bar babura da dama."
- Yahya Bagobiri
'Yan bindiga sun ji a jikinsu
Ya kara da cewa daga baya ’yan bindigan sun dawo da safe domin daukar gawarwakin ’yan uwansu tara da aka kashe.
“Ina so na yaba wa sojoji, domin sun kare yankin tare da hana ’yan bindigan haddasa babbar barna. Sun cancanci yabo, domin a wancan lokaci babu wanda ma zai iya fito wa daga gidansa."
- Yahya Bagobiri

Source: Original
Me hukumomi suka ce kan harin?
Da aka tuntube shi, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin Najeriya ta Brigade ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, sojojin sun kwato babura uku da wayoyin salula guda biyu masu dauke da alamar jini.
“Eh, ba zan iya tabbatar da ainihin adadin ’yan bindigan da aka kashe ba, amma wani dan sa-kai ya jikkata."
“Mun kwato babura uku da wayoyin salula guda biyu masu dauke da alamar jini."
- Kyaftin Babatunde Zubairu
'Yan bindiga sun sako mutane a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun sako wasu mutanen da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun saki mutanen ne bayan an kulla yarjejeniyar sulhu da su a karamar hukumar Malumfashi.
Zaman sulhun ya hada da shugaban karamar hukumar Malumfashi, masu rike da sarautun gargajiya da jagororin 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng


