Kwana 3 bayan Amurka Ta Kai Hari Sokoto, Shugaba Tinubu Ya Shilla Kasar Turai
- Shugaba Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa Turai kafin ya halarci wani taron kasa da kasa a Abu Dhabi bisa gayyatar da ya samu
- Taron na shekarar 2026 zai mayar da hankali kan haɗa fasahohin zamani, harkar kuɗi, da jama'a domin samar da bunƙasar kasashe
- Wannan ziyara na zuwa ne kwanaki uku bayan Amurka ta harba makamai a wasu sassan Najeriya, da zummar yaki da 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga birnin Lagos a ranar Lahadi zuwa nahiyar Turai a matsayin wani ɓangare na hutunsa na ƙarshen shekara.
Bayan isar Tinubu nahiyar Turai, ana sa ran shugaban kasar zai kuma zarce zuwa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Source: Twitter
UAE: Tinubu ya shilla zuwa kasar Turai
Shugaban kasar zai halarci wani taron ƙasa da ƙasa na shekarar 2026, wanda zai gudana a farkon Janairu, biyo bayan gayyatar da ya samu daga shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, in ji rahoton Punch.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, wannan taro zai haɗa shugabannin gwamnati, 'yan kasuwa, da ƙungiyoyin farar hula domin tattauna yadda za a ci gaba da samar da ci gaba mai dorewa a duniya.
Taron na shekarar 2026 mai taken "The Nexus of Next: All Systems Go," zai mayar da hankali kan haɗa fasahohin zamani, harkar kuɗi, da jama'a domin samar da bunƙasa. Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala taron.
Dambarwar hare-haren Amurka a Najeriya
Tafiyar Shugaba Tinubu na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Amurka ta kai wasu "munanan hare-hare" kan mayakan IS a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa shi ya ba da umarnin kai harin na ranar 25 ga Disamba a matsayin "kyautar Kirsimeti," ikirarin da ya saɓa wa kalaman jami'an Najeriya.
Rundunar sojin Amurka ta ce ta kai harin ne a sansanonin 'yan ta'adda da ke jihar Sokoto kusa da iyakar Nijar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi albishir ga 'yan Najeriya game da karbo wasu jiragen yaki daga Amurka

Source: Facebook
Halin da ake ciki a Sokoto, inda aka kai hari
Duk da cewa adadin mutanen da suka mutu bai fito fili ba, jami'an Amurka da na Najeriya sun tabbatar da kashe mayaka da dama.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya shaida wa BBC cewa wannan "aiki ne na haɗin gwiwa" kuma ba shi da alaƙa da wani addini ko ranar Kirsimeti, inda ya bayyana cewa an daɗe ana tsara harin ta hanyar amfani da bayanan sirri daga Najeriya.
Wani jami'in yankin Tangaza a jihar Sokoto, Isa Salihu Bashir, ya tabbatar da cewa harin ya lalata sansanonin 'yan ta'addan "Lakurawa" tare da kashe mayaka da dama.
Dajin da bama baman Amurka suka tarwatsa
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce hare-haren hadin gwiwa da Amurka sun tarwatsa sansanonin 'yan kungiyar IS a dajin Bauni da ke Tangaza.
Ministan yada labarai na kasa, Mohammed Idirs ya bayyana cewa an yi aikin ne bayan cikakken sahalewar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Mohammed Idris ya ce burbudin makaman da aka harba ne suka faɗa yankunan Jabo da Offa kuma babu fararen hula da suka rasa rai a sanadiyyar hakan.
Asali: Legit.ng

