Gwamna Abdulrazaq Ya ba 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Jihar Kwara Zabi 2

Gwamna Abdulrazaq Ya ba 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Jihar Kwara Zabi 2

  • Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya halarci bikin yaye sababbin jami'an tsaron dazuka da aka horas
  • Abdulrahman Abdulrazaq ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen kawo shirin samar da jami'an domin tunkarar matsalar rashin tsaro
  • Hakazalika, ya aika da sakon gargadi ga 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane wadanda ke addabar jihar Kwara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya aika da sakon gargadi ga ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ke aiki a jihar.

Gwamna Abdulrazaq ya gargade su da su fice nan take ko kuma su fuskanci hallaka, yana mai cewa gwamnati na amfani da dukkan hanyoyin da take da su domin kare lafiyar al’umma.

Gwamnan Kwara ya ja kunnen 'yan ta'adda
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Gwamna AbdulRazaq ya yi jawabi ne a ranar Asabar, 27 ga watan Disamban 2025 a Ilorin, babban birnin jihar, a wajen bikin yaye kusan sababbin jami'an tsaron dazuka 1,000 da aka horas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yaye jami'ai 7,000 a jihohin Arewa 7 domin inganta tsaro

Gwamnan ya bayyana shirin a matsayin wani babban sauyi da zai karfafa tsarin tsaron jihar.

Gwamna Abdulrazaq ya gargadi 'yan ta'adda

Ya ce za a tura akalla jami'an tsaron dazuka 200 a kowace karamar hukuma domin tsaron yankunan dazuzzuka tare da taimaka wa ’yan sa-kai na yankunan.

“Sakon a bayyane yake, fiye da kowane lokaci a baya, ’yan ta’adda yanzu suna da zabin barin jiharmu nan take ko kuma su fuskanci mummunan sakamako."

"Mun koma daukar matakin kai farmaki ne domin al’ummarmu sun cancanci samun zaman lafiya."

- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq

'Yan ta'adda za su ji ba dadi a Kwara

Gwamna AbdulRazaq ya kara da cewa wannan shiri zai tilasta wa masu laifi ko dai su gudu daga Kwara ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri.

“A yau mun bude sabon shafi a yakinmu da dukkan nau’ikan ta’addanci, satar mutane da hare-haren da wasu miyagun mutane ke kai wa al’ummarmu ta hanyar amfani da manyan yankunanmu domin nufin mugunta."

- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq

Kara karanta wannan

Sulhu ya yi rana: 'Yan bindiga sun sako mutanen da suka sace a Katsina

Gwamnan Kwara ya aika da sako mai zafi ga 'yan ta'adda
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na duba jami'an tsaron dazuka da aka yaye Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Source: Facebook

Gwamnan Kwara ya yabawa Shugaba Tinubu

Gwamnan ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tunani mai zurfi wajen kwato dazuzzukan Najeriya, korar masu laifi da kuma inganta tsaron jama’a.

Ya kuma yabawa hukumomin tsaro kan jajircewarsu, yana mai cewa jami'an tsaron dazuka da aka dauka, mafi yawansu daga al’ummomin yankuna za su yi aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaron da ake da su.

“Daukar makamai da horas da jami'an tsaron dazuka domin su cike gibin kokarin jami’an tsaro abin alfahari ne kuma wani babban sauyi ne."
"Wannan yana nuna a fili yadda gwamnati ta kuduri aniyar kawar da ta’addanci, ’yan bindiga da satar mutane a kasar nan."

- Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq

Ya bukaci mazauna jihar da su hada kai da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri, yana mai jaddada cewa samun hadin kan kowa, shi ne mabuɗin dorewar zaman lafiya.

PDP ta soki gwamnan jihar Kwara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan shingen binciken NSCDC, sun bude wa jami'ai wuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP a Kwara ta taso gwamnan jihar a gaba kan fashewar da ta auku a garin Offa.

Jam'iyyar PDP ta ce shiru da gwamnatin ta yi ya bar mazauna Offa cikin damuwa, tsoro da neman karin bayani kan abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng