Bayan Harin Amurka, Shehu Sani Ya Magantu kan Zuwan Rasha da China Najeriya
- Sanata Shehu Sani ya ce duk wani aikin soja da aka yi da yarda ko haɗin gwiwar gwamnati ba za a ɗauke shi a matsayin tauye ikon ƙasa ba
- Ya bayyana cewa ta’addanci ya daɗe yana tauye martabar ƙasa ta hanyar kisan jama’a, sace-sace da lalata rayuka a shiyyar Arewa maso Yamma
- 'Dan gwagwarmayar ya yi magana kan neman taimakon manyan kasashe kamar Rasha da China ko ma wasu kasashen da ke nahiyar Afrika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci kan harin da Amurka ta kai Najeriya, inda ya bayyana cewa matakin bai tauye ikon ƙasar ba muddin an yi shi da yarda ko da hannun gwamnatin Najeriya.
Ya ce Najeriya ta rasa daruruwan jaruman sojoji da dubban fararen hula, tare da kashe makudan kudi na tsawon kusan shekaru wajen yaƙi da ta’addanci, amma har yanzu matsalar na ci gaba.

Source: Facebook
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a X, yana mai cewa tsawon shekaru ‘yan ta’adda da gungun masu aikata laifuffuka sun riga sun take ikon ƙasa ta hanyar hallaka jama’a, ƙone ƙauyuka da sace ɗalibai.
Maganar Shehu Sani kan haɗin gwiwa
Shehu Sani ya ce idan aka yi la’akari da irin mummunan halin da yankin Arewa maso Yamma ya shiga, bai dace a ce aikin soja da aka yi da izinin gwamnati tauye ikon ƙasa ba ne.
A cewarsa, ‘yan ta’adda sun mai da yankin kamar filin jana’iza mara ƙarewa, inda ake cikin alhini da makoki a kai a kai. Ya ce an yi addu’a sosai da sulhu amma hakan bai kawo ƙarshen tashin hankalin ba.
Ya jaddada cewa dole ne a fuskanci ta’addancin da ƙarfin soja domin samun zaman lafiya, yana mai cewa ba za a iya dakile akidar tashin hankali da aikata laifuffuka ta hanyar sulhu kaɗai ba.
Maganar hada kai da Rasha da China
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ba Amurka kaɗai ba, duk ƙasar da ke son taimakawa Najeriya wajen kawar da ta’addanci ya kamata gwamnati ta marabce ta.
Ya ce idan China, Rasha ko wata ƙasar Afirka na da niyyar yin haɗin gwiwa don taimakawa Najeriya ta kawar da ‘yan ta’adda, to ya dace a buɗe ƙofofi gare su.

Source: Instagram
Shehu Sani ya yi amfani da misali inda ya ce idan gobara ta tashi a gida ko macizai suka shiga ɗaki, ba a da lokacin zaɓar wanda zai taimaka, abu mafi muhimmanci shi ne kashe gobarar ko kawar da barazanar.
Duk da goyon bayansa ga haɗin gwiwar ƙasashen waje, Shehu Sani ya jaddada cewa tushen tsaron Najeriya yana hannun rundunar sojin ƙasar da sauran hukumomin tsaro.
An kama babban dan bindiga a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun 'yan sandan Najeriya sun kama wasu manyan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Kwara.
Daya daga cikin wadanda aka kama shi ne dan bindiga da aka fi sani da Siddi da ke yawan bidiyo yana nuna kan shi a kafafen sada zumunta.
'Yan sanda sun samu mai garkuwa da mutanen da babur guda daya, bindiga kirar AK-47, tarin harsashi da kuma wasu makudan kudi.
Asali: Legit.ng


