Tambawul Ya Aika Sako ga Mutanen Sokoto bayan Harin Amurka a Najeriya

Tambawul Ya Aika Sako ga Mutanen Sokoto bayan Harin Amurka a Najeriya

  • Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi tsokaci kan hare-haren sama da Amurka ta kawo a jiharsa ta Sokoto
  • Aminu Waziri Tambuwal ya jaddada muhimmancin kare rayukan fararen hula tare da kira ga jama'a su bayar da hadin kai
  • Tsohon gwamnan ya kuma bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu yayin da hukumomin da suka dace ke ci gaba da gudanar da ayyukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Sanata Aminu Tambuwal (mai wakiltar Sokoto ta Kudu) ya yi martani kan hare-haren da Amurka ta kai a jiharsa.

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira da a kwantar da hankula a jihar Sokoto bayan hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai a ranar Kirsimeti.

Tambuwal ya yi magana kan harin Amurka
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Tambuwal ya bukaci a kare fararen hula

Tambuwal ya jaddada muhimmancin kare lafiyar fararen hula, tare da yin kira ga hadin kan al’umma a daidai lokacin da ake samun rahotannin yiwuwar samun asarar rayuka.

“Ina sane da rahotannin da suka shafi wani harin sama da aka kai a matsayin wani bangare na yaki da ta’addanci da ake gudanarwa ta hadin gwiwar gwamnatin tarayya ta Najeriya da Amurka."
"Ina kira ga al’ummarmu da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka yayin da hukumomin da suka dace ke fayyace cikakkun bayanai game da wannan aiki."
“Ina kuma so na tabbatar wa al’ummar Sokoto ta Kudu cewa ina tattaunawa kai tsaye da hukumomin tsaro da suka dace domin samun cikakken bayani da kuma tabbatar da cewa an kiyaye dukkan matakan kariya da suka wajaba."

- Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya kwantar da hankulan jama'a

Tambuwal ya ce yana da matukar muhimmanci a kwantar wa jama’a da hankali cewa ayyukan yaki da ta’addanci na nufin murkushe ’yan ta’adda da masu aikata laifuka ne da ke barazana ga tsaron jama’a baki daya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

Ya ce ayyukan ba suna nufin shafar fararen hula marasa laifi ba, wadanda su ma suke fama da matsalar rashin tsaro.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya ce kare rayukan fararen hula shi ne abu mafi muhimmanci kuma ginshiki a duk wani sahihin aikin tsaro.

Tambuwal ya yabawa sojojin Najeriya

Ya yaba da jarumtaka da kwarewar sojojin Najeriya da jami’an tsaro, wadanda ke ci gaba da aiki tukuru tare da hadin gwiwar abokan hulda na kasa da kasa domin yaki da ta’addanci da ’yan bindiga a cikin mawuyacin yanayi.

A cewarsa, sadaukarwa da jajircewarsu wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali sun cancanci cikakken goyon baya da hadin kai daga al’umma.

Tambuwal ya bukaci a kwantar da hankula kan harin Amurka
Sanata Aminu Waziri Tambuwal mai wakiltar Sokoto ta Kudu J Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya da mazauna yankuna da su ci gaba da yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai da kuma gujewa yada labaran karya da ka iya kara tayar da fargaba ko tashin hankali.

Tambuwal ya ce yana da yakinin cewa ta hanyar hadin kai, sa ido da goyon baya ga ayyukan tsaro, ’yan Najeriya za su yi galaba a kan ’yan ta’adda tare da tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar Sokoto da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Halin da mazauna kauyen Sokoto ke ciki a yanzu bayan harin Amurka

Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da harin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta yi magana kan hare-haren sama da Amurka ta kawo.

Gwamnatin ta bayyana cewa an yi aikin ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin sojojin Amurka da na Najeriya domin dakile barazanar tsaro a yankin.

Hakazalika ta jaddada cewa harin da aka kai a yankin Jabo bai yi sanadin mutuwa ko jikkata fararen hula ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng