Hukumar INEC Ta Amince da Rijistar Sababbin Jam'iyyun Siyasa 2 a Najeriya
- Hukumar INEC ta sake soke bukatar kungiyoyi shida da suka nemi yin rijistar zama jam'iyyun siyasa a Najeriya
- Wasu majiyoyi sun bayyana cewa INEC ta amince da kungiyoyi biyu kacal zuwa matakin karshe na yin rijista
- Sai dai wasu daga cikin kungiyoyin da suka nemi rijistar zama jam'iyyun sun sha alwashin kalubalantar matakin INEC a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da ƙungiyoyin siyasa biyu kacal, AAP da DLA, su wuce zuwa matakin ƙarshe na rajistar zama jam’iyyun siyasa.
A watan Yunin 2025, INEC ta bayyana cewa ta karɓi buƙatu daga ƙungiyoyi 110 da ke son yin rajista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta tattaro cewa zuwa farkon watan Satumba 2025, adadin ya ƙaru zuwa ƙungiyoyi 171, sakamakon ƙarin buƙatu da aka shigar.
INEC ta zabi kungiyoyi 14 a matakin farko
A ranar 11 ga Satumba, INEC ta zabi ƙungiyoyi 14 daga cikin ƙungiyoyi 171 da suka nemi rajista.
Daga bisani, a watan Oktoba, hukumar ta sake taƙaita jerin ƙungiyoyin zuwa takwas, bayan ta tabbatar sun cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki.
Ƙungiyoyin da suka tsallaka zuwa wannan mataki sun haɗa da: ADA, CDA, ASP, AAP, DLA, GFP, NDP da PFP, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
INEC ta soke bukatar ƙungiyoyi shida
Sai dai majiyoyi masu masaniya kan lamarin sun bayyana cewa bayan sake tantancewa da INEC ta yi, ƙungiyoyi biyu, AAP da DLA, ne suka cika dukkan sharuddan ƙarshe.
INEC ta ambaci matsalar adireshin ofishi a matsayin ɗaya daga cikin dalilan soke rajistar daya daga cikin kungiyoyi shida da aka soke bukatar su ta neman zama jam'iyyun siyasa.
Sai dai ƙungiyar ta musanta zargin, tana mai cewa ta sanar da INEC sauyin adireshi tun da wuri, ta kuma sanya sababbin bayanai a shafin yanar gizon hukumar.
"Jami’an INEC sun ma je wurin domin tantancewa ba tare da sun nuna wata matsala a wancan lokacin ba,” in ji majiyar.

Source: Twitter
Ana shirin maka INEC a gaban kotu
Wani mamba daga cikin ƙungiyoyin da aka soke bukatarsu ta rijistar zama jam'iyya ya ce INEC ta yi ikirarin cewa ba ta da wasu takardu ko bayanai da ƙungiyoyin suka ce sun miƙa mata tun da farko.
A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ƙungiyoyin da aka soke suna shirin kalubalantar matakin INEC a kotu.
INEC ta fara kokarin sulhunta PDP
A baya, kun ji cewa hukumar INEC ta fara kokarin samar da masalaha da sulhu tsakanin bangarorin jam'iyyar PDP da ke adawa da juna.
Jam'iyyar PDP dai ta jima tana fama da rigingimu kala daban-daban, amma a baya-bayan nan, kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya dare gida biyu.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) ya ce an kira wannan zama ne bayan "wasiku masu karo da juna" da hukumar ta samu daga PDP.
Asali: Legit.ng

