'Yan Sanda Sun Yi Gaba da Gaba da Masu Garkuwa da Mutane a Ranar Kirsimeti

'Yan Sanda Sun Yi Gaba da Gaba da Masu Garkuwa da Mutane a Ranar Kirsimeti

  • Jami'an 'yan sandan sun ceto Geoffrey Akume, wani mutumi da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Kirsimeti a Benue
  • Masu garkuwar sun ranta na kare bayan sun ji karar motar 'yan sanda, wanda hakan ya ba da damar ceto wanda aka sace lami-lafiya
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar ya tabbatar da cewa ba a biya kudin fansa ba, sannan ya bukaci jama'a su kara sa ido kan tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Rundunar ’yan sanda ta jihar Benue ta yi nasarar dakile yunƙurin yin garkuwa da mutane a ranar Kirsimeti, tare da ceto wani mutumi mai suna Geoffrey Akume.

Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, wadda aka bai wa manema labarai a Makurdi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan shingen binciken NSCDC, sun bude wa jami'ai wuta

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane a Benue
Jami'an rundunar 'yan sanda za su fita bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun dakile shirin 'yan bindiga

DSP Edet ta ce 'yan sanda sun fafata da 'yan bindigar ne da sanyin safiyar ranar a yankin Tiortu, da ke kan titin Gboko–Makurdi, in ji rahoton Punch.

Ta bayyana cewa wanda aka ceto yana kan hanyarsa daga Gboko zuwa Makurdi lokacin da wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka tare shi a Tiortu.

A cewarta, sun yi amfani da ƙarfi suka sace shi, suna shirin kai shi cikin wani daji mai yawan bishiyoyi da duwatsu da ke kusa da wurin.

“Rundunar ta samu rahoton neman ɗauki, wanda ya sa jami’an ’yan sandan Benue suka kai dauki nantake, suka fara sintiri mai tsanani tare da gudanar da bincike a yankin.

An kubutar da wanda aka sace

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“A lokacin da maharan suka hango tawagar ’yan sanda, sai suka yi kokarin mayar da martani amma daga bisani suka jefar da wanda suka sace suka tsere cikin daji.

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto

“Tawagar sintirin ta samu nasarar ceto mutumin, wanda ya kuɓuta daga hannun masu garkuwar ba tare da ya ji rauni ba, kuma babu ko sisi da aka biya a matsayin kudin fansa.
“Daga bisani an kai shi ofishin ’yan sanda na Abinse, inda Kwamishinan ’yan sanda na jihar ya yi masa tambayoyi, sannan aka haɗa shi da iyalansa,” ta ƙara da cewa.

Edet ta ce kwamishinan ’yan sanda, CP Ifeanyi Emenari, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin bisa saurin daukar mataki, jarumta da kwarewa.

'Yan sanda sun dakile shirin garkuwa da wani mutumi a Benue.
Taswirar jihar Benue da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun ba al'ummar Benue tabbaci

Emenari ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Benue kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman a wannan lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Ya kuma bayyana cewa an ƙara yawan sintiri, binciken ababen hawa da mutane, da kuma aikin tsaro bisa bayanan sirri a muhimman wurare a fadin jihar.

“An shawarci jama’a da su kasance masu sa ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko aiki da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta hanyoyin gaggawa da aka amince da su."

- CP Ifeanyi Emenari

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com