Sarki Sanusi II Ya Girgiza kan Mutuwar 'Yan Majalisar Kano 2 a Rana Guda

Sarki Sanusi II Ya Girgiza kan Mutuwar 'Yan Majalisar Kano 2 a Rana Guda

  • Masarautar Kano ta miƙa sakon ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokoki bisa rasuwar ’yan majalisa biyu a rana day
  • Rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji da Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo ba zato ba tsammani ta jefa majalisar dokokin Kano cikin alhini da jimami
  • Masarautar ta yabawa gudunmawar marigayan tare da roƙon Allah Ya gafarta musu Ya kuma bai wa al’umma haƙurin jure rashinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba, Khalifa Muhammad Sanusi II, PhD, CON, ta bayyana alhini bisa rasuwar ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu.

A cikin wata sanarwa, Masarautar ta miƙa sakon ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano, Majalisar Dokokin Jihar, da daukacin al’ummar Kano, tana mai bayyana wannan lamari a matsayin babban rashi.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba ya ce bayan samun labarin rasuwar 'yan majalisa 2 a Kano

Sarki Muhammadu Sanusi II
Sanusi II na zaune a fadarsa a Kano. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanin masarautar Kano ne a wani sako da shafin Sarki Sanusi II ya wallafa a kafar Facebook.

Marigayan da abin ya shafa sun haɗa da Hon. Sarki Aliyu Daneji, wakilin Kano Municipal, da kuma Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, wakilin Ungoggo.

Sakon Sanusi II kan rasuwar 'yan majalisa 2

Masarautar Kano ta bayyana cewa ta shiga jimami da alhini matuƙa sakamakon wannan rashi, tare da jaddada irin gudunmawar da marigayun suka bayar wajen hidimar al’umma da ci gaban jihar Kano.

A cewar sanarwar, Masarautar ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayun, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu, kuma Ya bai wa iyalansu, ’yan Majalisa da al’ummar Jihar Kano haƙurin jure wannan babban rashi.

Masarautar ta kuma nuna cewa rasuwar mutanen biyu a lokaci ɗaya ta bar babban gibi a harkokin siyasa da wakilcin jama’a a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya yi alhinin rasuwar 'yan majalisar dokoki 2 a jihar Kano

Alhini a Majalisar Dokokin Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shiga yanayin jimami bayan samun labarin rasuwar ’yan majalisar biyu, wadanda aka ce sun rasu a rana daya.

Rahotanni sun nuna cewa Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar kan kasafin kuɗi, shi ne ya fara rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya.

Abba Kabir da 'yan majalisar da suka rasu
Gwamnan Kano da 'yan majalisar da suka rasu. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wasu bayanai sun tabbatar da cewa Hon. Ungogo ya rasu ne a harabar Majalisar Dokokin Jihar Kano yayin da yake kan bakin aiki.

Har ila yau, rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji, wakilin Kano Municipal, ta ƙara tsananta yanayin makoki, inda ake ganin cewa Majalisar da al’ummar Kano sun yi babban rashi na wakilai biyu masu muhimmanci a lokaci guda.

Barau ya zargi Abba da take hakki

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Barau Jibrin ya zargi Abba Kabir Yusuf da take hakkin Fa'izu Al-Fikindi.

Rahotanni sun nuna cewa Barau ya ba tsohon shugaban karamar hukuma, Al-Fikindi, Naira miliyan 7 da ya ce Abba ya hana shi.

Yayin da ya ke martani, Al-Fikindi ya ce ya riga ya san dama jam'iyyar APC ba za ta bar shi a baya ba lura da abin da aka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng