An Baza 'Yan Sanda Ta ko ina a Maiduguri bayan Harin Bam a Masallaci
- Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kara tsaurara tsaro bayan tashin bam a masallacin Al-Adum da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri
- An tura sama da jami’ai 1,000 domin tabbatar da tsaron wuraren ibada, manyan tituna da wuraren taruwar jama’a a lokacin bukukuwa
- ’Yan sanda sun bukaci al’umma su ci gaba da harkokinsu cikin natsuwa tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta sanar da tura jami’ai sama da 1,000 a fadin Maiduguri da wasu muhimman wurare bayan fashewar bam a wani masallaci da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.
Lamarin ya faru ne da dare a masallacin Al-Adum da ke yankin kasuwar Gamboru, yayin da masu ibada ke gudanar da sallar Magariba.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Daso ya ce an tsananta matakan tsaro ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman a wannan lokaci na bukukuwa da cunkoso.
An tsaurara matakan tsaro a Maiduguri
Da yake magana, ASP Daso ya ce duk da cewa an riga an kafa wasu tsare-tsaren tsaro kafin faruwar lamarin, rundunar ta ga dacewar kara daukar matakai masu tsauri bayan abin da ya faru.
Ya ce rundunar za ta tabbatar da mamaye wuraren ibada, manyan tituna, wuraren shakatawa da sauran wuraren da ake sa ran taruwar jama’a da yawa.
Vanguarda ta rahoto ya ce jami’an tsaro za su kasance a shirye domin dakile duk wani yunkuri da ka iya barazana ga zaman lafiya.
Daso ya kara da cewa za a yi hadin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da cewa an rufe dukkan wuraren da ka iya zama barazana.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Bam ya tashi da mutane a masallaci ana sallar Magarib a Maiduguri
An tura 'yan sanda 1,000 Maiduguri
Kakakin ’yan sandan ya bayyana cewa aikin tsaron na hadaka ne tsakanin rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da na bayar da agajin gaggawa.
Ya ce tura jami’ai sama da 1,000 a cikin Maiduguri kadai na nuni da yadda gwamnati ke daukar lamarin tsaro da muhimmanci.
A cewarsa, wannan tsari zai taimaka wajen hana kai hare-hare, da kuma ba wa jama’a kwarin gwiwar ci gaba da gudanar da rayuwarsu ba tare da tsoro ba.

Source: Facebook
Daso ya bayyana cewa an tanadi motocin sintiri da jami’an sa-kai domin rika zagayawa a yankuna masu hadari, tare da sanya ido kan duk wani motsi da bai dace ba.
Rundunar ’yan sandan ta bukaci mazauna Maiduguri da sauran sassan jihar Borno su ci gaba da harkokinsu na halal, amma su kasance masu taka-tsantsan da lura da muhallinsu.
Maganar sojoji kan hari bam a masallaci
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi karin haske game da harin da aka kai wani masallaci a jihar Borno.
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun bayyana cewa 'yan kungiyar Boko Harama ake zargi da kai harin kunar bakin waken.
Rahotanni daga rundunar soja sun ce bam din ya kashe wasu mutane nan take a masallacin yayin da wasu suka rasu a asibiti.
Asali: Legit.ng

