Sheikh Pantami Ya Yi Magana Mai Jan Hankali kan Tashin Bam a Wani Masallaci a Maiduguri

Sheikh Pantami Ya Yi Magana Mai Jan Hankali kan Tashin Bam a Wani Masallaci a Maiduguri

  • Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wani masallacin Juma'a a Maidugurin jihar Borno
  • Fitaccen malamin addinin musulunci ya jajantawa wadanda harin ya shafa, gwamnati da daukacin al'ummar jihar Borno
  • Farfesa Pantami ya roƙi Allah Ya tona asirin masu aikata wannan ta’asa, Ya hukunta su, tare da kawo dorewar zaman lafiya a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Pantami, ya jajantawa al'ummar jihar Borno bisa ibtila'in harin bam da aka kai masallaci a Maiduguri.

Pantami ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin Borno da al’ummar jihar baki ɗaya, bisa harin bam da ya afku a Masallacin Juma’a na Al-Adum, da ke kusa da kasuwar Gamboru.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya yi alhinin rasuwar 'yan majalisar dokoki 2 a jihar Kano

Sheikh Pantami.
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Babban malamin addinin musulunci ya mika sakon jaje ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Alhamis, 25 ga watan Disamba, 2025.

An tashi bam a masallacin Borno

Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda wani dan kunar bakin wake ya kutsa masallacin, ya tashi bam ana cikin sallar Magariba a Maiduguri.

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Borno ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce mutum biyar sun mutu yayin da wasu sama da 30 suka samu raunuka.

Pantami ya bayyana cewa ya samu labarin lamarin cikin tsananin baƙin ciki, inda harin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 24 ga Disamba, 2025, yayin da ake gudanar da sallar Magariba.

Pantami ya yi tir da harin masallaci

A cewarsa, harin wanda ya auku a wuri mai tsarki da kuma a lokacin ibada, ya yi sanadin rasa rayukan bayin Allah da dama tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fitar da bayanai kan harin bam a masallacin Maiduguri

Pantami ya ce:

“Wannan mummunan hari ne kai tsaye ga bil’adama baki ɗaya, kuma ya saɓa wa koyarwar Musulunci da ke kare rayuwa da amincin masu ibada.”

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da wadanda suka jikkata, tare da gwamnati da al’ummar Jihar Borno.

Tsohon ministan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus, tare da bai wa waɗanda ke karɓar magani cikakkiyar lafiya.

Sheikh Pantami ya yaba wa jami'an tsaro

Haka kuma, Pantami ya yaba wa jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya bisa gaggawar da suka yi wajen tunkarar lamarin da ceto rayuka.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu taka-tsantsan, wayar kai da haɗin kai da hukumomin tsaro, musamman a wannan lokacin bukukuwa da ake yawan tafiye-tafiye da tarurruka.

Jihar Borno.
Taswirar jihar Borno a Najeriya Hoto: legit.ng
Source: Original

A ƙarshe, Farfesa Pantami ya roƙi Allah Ya tona asirin masu aikata wannan ta’asa, Ya hukunta su, tare da kawo dorewar zaman lafiya da tsaro ga Maiduguri, Jihar Borno da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bam ya tashi da mutane a masallaci ana sallar Magarib a Maiduguri

Sojoji sun tabbatar da tashin bam a Masallaci

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin bam masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri yayin sallar Magariba.

Jami’in yada labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa rundunar sojin ta samu rahoton ne a lokacin da ake tsaka da sallar Magariba.

A cewarsa, binciken farko-farko ya nuna cewa wani da ake zargin dan kungiyar Boko Haram ne ya kai harin ta hanyar tayar da bam din da ya daura a jikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262