Tashin Hankali: Gobara Ta Kama Gini Mai Hawa 22, Akwai 'Yan Kasuwa a ciki
- Gobara ta tashi a ginin Great Nigeria Insurance House mai hawa 22 a Legas, inda ta lakume ofisoshi da wurin adana kayan tufafi
- Kafin jami'an kashe gobara su isa, wutar ta riga ta bazu zuwa hawa na biyar da na shida, inda ta yi barazanar cinye daukacin ginin
- Hukumar kashe gobara ta yi dakile wutar daga bazuwa zuwa gine-ginen Radio Nigeria da Oluwole Plaza bayan aikin tsawon sa'o'i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Masu aikin ceto da kashe gobara sun fafata da wata mummunar gobara da ta barke a sanannen ginin nan mai suna Great Nigeria Insurance House, wanda yake kan titin Martins a jihar Lagos.
Ginin, wanda aka fi sani da wurin ajiyar tufafi da masana'antu, ya kama da wuta ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, inda hayaki ya turnuke a sararin samaniyar yankin na Oluwole.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Bam ya tashi da mutane a masallaci ana sallar Magarib a Maiduguri

Source: UGC
Gobara ta tashi a gini mai hawa 22
Babban sakataren hukumar kiyaye haɗurra ta jihar Lagos (LASEMA), Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin, a cewar rahoton Punch.
Jaridar ta rahoto Dokta Olufemi ya bayyana cewa wutar ta samo asali ne daga ɗaya daga cikin ofisoshin da ke hawa na huɗu na ginin mai hawa 22.
Kafin jami'an kashe gobara su isa, wutar ta riga ta bazu zuwa hawa na biyar da na shida, inda ta yi barazanar cinye daukacin ginin da kuma masallacin da ke kusa da wurin.
A cewarsa, har yanzu ba a tantance musabbabin gobarar ba, sai dai ta fara ne daga bene na huɗu kafin ta bazu zuwa sauran benaye.
Oke-Osanyintolu ya ce:
“Da isar tawagar Shark Response wurin, mun tarar da gini mai hawa 22, watau Great Nigeria Insurance House, yana ci da wuta.
“An shawo kan gobarar da ta bazu zuwa masallaci, sannan an yi nasarar ceto mafi yawan sassan Oluwole Plaza, tare da kashe wutar gaba ɗaya.”
Adadin wadanda suka raunata a gobara
Duk da cewa ba a rasa rai ba a cikin wannan hatsari, mutane bakwai ne suka samu raunuka daban-daban na ƙonewa, inda jami'an lafiya suka ba su taimakon gaggawa kafin a garzaya da su asibiti.
Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa maza bakwai manya sun samu raunukan ƙonewa daban-daban, inda jami’an lafiya suka ba su kulawar gaggawa kafin a kai su asibitoci da ke kusa.
Ya kuma ce maza uku da mata biyu sun samu shakar hayaƙi, an yi musu magani a wurin kafin a sallame su, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Source: Twitter
Hukumomi sun hana gobarar yaduwa
Shugabar hukumar kashe gobara ta jihar Lagos, Margaret Adeseye, ta bayyana cewa dakarunsu sun yi kokari wajen ganin wutar ba ta bazu zuwa wasu gine-ginen ba.
Ta lura cewa ginin ya ƙunshi rumbunan adana kaya ne, musamman tufafi, wanda hakan ya sa wutar ta ƙara ƙarfi cikin ƙaramin lokaci.
Sai dai, jami'an sun samu nasarar kare ginin Radio Nigeria da ke kusa da wannan bene mai hawa 22, kuma ana ci gaba kokrin tabbatar da cewa wutar ba ta sake tashi ba.
Gobara ta tashi a gidan Ahmad Makarfi
A wani labari, mun ruwaito cewa, gobara ta tashi a Asokoro, Abuja, inda ta lalata gidaje huɗu da ke a wuri daya, bayan wuta ta fara ci daga farantan solar a saman gini.
Hukumar kai daukin gaggawa ta FEMD ta tabbatar da cewa gidan da gobarar ta babbake yana da alaƙa da tsohon gwamnan Zamfara,Sanata Ahmed Yerima.
Masani, Gaddafi Abubakar ya ce ana samun gobara daga farantan solar sakamakon amfani da kaya marasa inganci, katsewar wayoyi ko aikin wadanda ba su kware ba.
Asali: Legit.ng

