Bincike: Dagaske Musulmin Najeriya ba Za Su Biya Sabon Haraji a 2026 ba? An Samu Bayani

Bincike: Dagaske Musulmin Najeriya ba Za Su Biya Sabon Haraji a 2026 ba? An Samu Bayani

Plateau, Nigeria - Wani malamin majami'a a jihar Filato, Fasto Ezekiel Dachomo na neman tayar da kura kan sababbin dokokin haraji da za su fara aiki a farkon shekarar 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Fasto Ezekiel Dachomo ya fito ya yi ikirarin cewa sababbin dokokin haraji da gwamnatin tarayya ta kafa za su shafi Kiristoci ne kaɗai, amma ban da Musulmai a Najeriya.

Haraji.
Gwamnatin tarayya za ta fara aiwatar da dokokin haraji a farkon 2026 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ikirarin da wani fasto ya yi a Filato

Malamin addinin kiristan ya faɗi hakan ne a yayin wani shirin tattaunawa mai suna Lucky Udu Experience da aka wallafa a manhajar Youtube.

A cewarsa, a ƙarƙashin sauye-sauyen haraji da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinhbu ya rattaba wa hannu, Kiristoci ne kawai za su riƙa biyan haraji, yayin da ya ce Musulmi ba za su biya ba.

Kara karanta wannan

Matasan ADC sun tsunduma zanga zanga kan dokokin harajin Tinubu

Ya ce,

“Sun ce daga shekara mai zuwa za a fara biyan haraji. Na gaya wa ‘yan’uwanmu Kiristoci cewa wannan harajin, mu ne za mu biya shi. Amma idan ana maganar Musulmi, ba za su taɓa biyan wannan haraji ba.”

Game da sabbin dokokin haraji

A ranar 9 ga Satumba, gwamnatin tarayya ta fitar da sababbin dokokin gyara tsarin haraji na ƙasa, waɗanda aka tsara za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Sababbin dokokin sun haɗa da Dokar Harajin Najeriya, NTA ta 2025, Dokar Gudanar da Haraji, NTAA ta 2025, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya, NRSEA ta 2025 da kuma Dokar Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Haraji, JRBEA, ta 2025.

A ranar 4 ga Oktoba, Shugaban Kwamitin Gyaran Haraji na Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce ya rataya a wuyan duk wani ɗan Najeriya ya bayyana adadin kuɗin shigar da yake samu domin biyan haraji.

Ya ce wannan wajabci na bayyana kudin shiga ba sabon abu ba ne, doka ce da ta daɗe tana aiki, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Tinubu da tawagar Haraji.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da shugaban kwamitin gyara tsarin haraji, Taiwo Oyedele Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Oyedele ya ce:

“Duk wanda ke samun kuɗi, ko waye shi, yana da alhakin bayyana kudin da yake samu ta hanyoyin da suka dace.
"Sai dai dokar ta kebe wasu mutane daga biyan haraji, ciki har da waɗanda ke samun ƙasa da N250,000 a wata, tare da rangwame ga masu ƙaramin ƙarfi da ƙananan ‘yan kasuwa.

Duk da haka, ba a tanadi wata doka da ta ware mutane ta dauke musu biyan haraji bisa addini ba, ko Kirista ko Musulmi.

Hukuncin karshe kan ikirarin

Babu wata hujja da ke tabbatar da ikirarin Fasto Dachomo. Sababbin dokokin haraji ba su ware Musulmi daga biyan haraji ba.

A ƙarƙashin dokokin gyaran haraji na Najeriya, duk wanda doka ta ɗauka a matsayin mai biyan haraji, daidaikun mutane ko kamfanoni, wajibi ne ya biya, ba tare da la’akari da addininsa ba.

Ndume ya bukaci a dakatar da dokokin haraji

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da aiwatar da sababbin dokokin haraji saboda zarge-zargen da suka taso.

Kara karanta wannan

"Na cancanci zama shugaban Najeriya," Gwamna ya yi magana kan yin takara a 2027

Sanata Ndume ya bukaci Tinubu da ya kafa wani kwamiti na musamman don gano gaskiyar zargin canza fasalin dokokin harajin da majalisar tarayya ta amince da su.

Wannan dai na zuw ane bayan an yi zargin cewa akwai banbanci a tanade-tanaden dokokin harajin da ke hannun gwamnati da wanda Majalisa ta yi karatu har ta amince da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262