Gwamna Uba Sani Ya Kafa Sabon Tarihi bayan Sanya Hannu kan Kasafin Kudi a Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Kafa Sabon Tarihi bayan Sanya Hannu kan Kasafin Kudi a Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kudi ta shekarar 2026 da ke shirin kamawa
  • Uba Sani ya ware kaso mai tsoka ga bangaren ilmi a cikin kasafin kudin wanda ya rattabawa hannu a ranar Litinin, 22 ga watan Disamban 2025
  • A cikin kasafin kudin, Gwamna Uba Sani, ya ware wasu kudade wadanda ba a taba ware irin su ba a tarihin jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani ya ware Naira miliyan 100 ga kowace mazaba cikin guda 255 da ake da su a jihar Kaduna cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Matakin da Gwamna Uba Sani ya dauka shi ne irinsa na farko a tarihin jihar, kuma ya yi daidai da kudurin gwamnan na bunkasa ci gaban al’umma daga tushe.

Kara karanta wannan

'Ba mu bukatar taimakon azzalumai': Gumi ya soki Amurka kan hari a Sokoto

Gwamna Uba Sani ya kafa tarihi a jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce kwamishinan tsare-tsare da kasafi, Hon. Mukhtar Ahmed Morovia, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ranar Laraba, 24 ga watan Disamban 2025.

Uba Sani ya sanya hannu kan kasafin kudi

An yi taron ne bayan rattaba hannu kan dokar kasafin kuɗi ta 2026, inda ya yi bayani dalla-dalla kan kasafin kudin.

Idan za a tuna cewa Gwamna Uba Sani ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin 2026 a ranar Litinin, 22 ga watan Disamban 2025.

Bangaren ilimi ya samu kaso mafi girma, wato kashi 25 cikin 100 na jimillar Naira biliyan 985.9 na kasafin kuɗin jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya ware kudi ga mazabu

Da yake gabatar da rabon kasafin, kwamishinan ya ce Naira miliyan 100 da aka ware ga mazabu 255 na daga cikin jajircewar gwamnan wajen kawo ci gaba ga kowa da kowa da kuma inganta rayuwar al’umma a matakin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnoni 19 suka ce kan bam din da ya tashi a masallacin Juma'a a Maiduguri

Ya ce za a rarraba kuɗaɗen cikin gaskiya da adalci, inda al’ummomi da kansu za su yanke shawarar ayyukan da suke so ta hannun kwamitocin ci gaban mazabu, jaridar Vanguard ta dauko labarin.

A cewarsa, an ware Naira miliyan 100 ɗin ne domin ayyuka a fannonin lafiya, ilimi, noma da walwalar al’umma, kuma za a aiwatar da su ta hannun ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassa daban-daban da abin ya shafa.

Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani, wanda ke sahun gaba wajen goyon bayan haɗin kai da daidaito, ya fahimci muhimmancin ci gaban al'umma wajen samun ci gaban jihar gaba ɗaya.

Gwamna Uba Sani ya sanya hannu kan dokar kasafin kudi
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

A cewarsa, gwamnan na da kudurin tabbatar da daidaitaccen ci gaba, inda ba za a bar wata al’umma a baya ba.

Daga cikin mambobin majalisar zartarwa ta jihar da suka halarci taron akwai kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Ahmed Maiyaki, kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo da kwamishinan noma, Murtala Dabo.

Sauran sun hada kwamishinan muhalli da albarkatun kasa, Alhaji Abubakar Buba, kwamishiniyar kasuwanci, Misis Patience Fakai, kwamishinan harkokin jin-kai, Barde Yunana Markus.

Shiri ne mai kyau

Wani mazaunin Kaduna, Mahmud Auwal, ya shaidawa Legit Hausa cewa tsarin da Gwamna Uba Sani ya fito da shi abu ne mai kyau.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi jiha 1 da za ta iya tatso Naira tiriliyan 1 daga gidaje duk shekara

"Tabbas idan har aka saki kudaden kamar yadda aka sanya a kasafin kudin, za su yi amfani sosai. Za a gudanar da muhimman abubuwa da su."
"Muna fatan idan an fitar da kudaden, a yi amfani da su yadda ya dace."

Mahmud Auwal

Uba Sani ya tsawaita lokacin yin ritaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi wa malaman makaranta babban gata.

Gwamna Uba Sani ya tsawaita lokacin yin ritaya ga malaman makaranta daga shekara 60 zuwa shekara 65.

Hakazalika, gwamnan ya fito da tsarin ba da alawus ga malamai da aka tura zuwa yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng