Wata Sabuwa: Kalaman Kwankwaso kan Masarautar Kano Sun Tayar da Kura
- Batun rikicin masarautar Kano na ci gaba da jawo cece-kuce bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wasu kalamai
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bukaci kwamishinan 'yan sanda da ya janye jami'an tsaron da ke fadar Sarki Aminu Ado Bayero
- Sai dai, kalaman na Kwankwaso sun jawo martani mai zafi daga wajen Aminu Babba Dan'agundi wanda ke kusa da Sarkin Kano na 15
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da ya yi kira ga ’yan NNPP da su nuna biyayya ga Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Kalaman na Kwankwaso sun haifar da sabon ce-ce-ku-ce tare da martani mai zafi daga Sarkin Kano na 16, Aminu Ado Bayero.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce wani babban mai rike da sarauta a Kano, Aminu Babba Dan'agundi, ne ya yi martani ga tsohon gwamnan na Kano.
Ana takaddama kan sarautar Kano
A ranar 23 ga Mayu, 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Aminu Ado Bayero daga sarautar Kano bayan majalisar dokokin jihar Kano ta soke dokar majalisar sarakunan jihar ta 2019, wadda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kafa.
Idan ba a manta ba, sabuwar dokar ta maido da Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Sai dai, Aminu Ado Bayero ya kalubalanci matakin gwamnati a kotu, kuma har yanzu yana gudanar da harkokinsa daga karamar fada da ke Nasarawa GRA a cikin birnin Kano.
Me Kwankwaso ya ce kan sarautar Kano?
Da yake jawabi a ranar Talata a wajen kaddamar da tsaron Kano ta NWC, Kwankwaso ya bukaci mambobin Kwankwasiyya da su tsaya tsayin daka kan abin da ya kira yunkurin gwamnatin tarayya na tilasta Aminu Ado Bayero a matsayin sarki.
A wajen taron wanda Sanusi II ya halarta, Kwankwaso ya bukaci kwamishinan 'yan sandan Kano ya janye jami'an tsaro daga fadar Aminu Ado Bayero, inda ya ce zamansu na kara tayar da hankula.
An yi wa Kwankwaso martani mai zafi
A martanin da ya yi, Aminu Babba Dan’agundi, ya yi Allah-wadai da kalaman Kwankwaso, yana mai cewa kalaman tayar da fitina ne da kuma raina kotu.
Da yake magana da Lumana Radio International, Dan’agundi ya ce Ado Bayero bai karya wata doka ba da ya ci gaba da zama a karamar fadar.

Source: Facebook
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta hana Sarki Aminu damar samun adalci kafin yanke hukunci a kansa.
"Muna kalubalantar matakin gwamnatin jihar a kotu. Kotu ta riga ta yanke hukunci cewa sauke sarkin ba bisa ka’ida ba ne, kuma ta umarce shi da ya ci gaba da zama.”
"Ko ba tare da ’yan sanda ba, muna da ikon tattara dubban matasa domin kare fadar. Idan sarauta zabe ce, za mu doke Kwankwaso da tawagarsa ba tare da wata shakka ba."
- Aminu Babba Dan'agundi
Dan’agundi ya kuma yi kira ga magoya baya da su kwantar da hankalinsu, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa Aminu Ado Bayero zai dawo kan karagar sarauta gaba ɗaya nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya mika bukata ga yan sanda kan zaman Aminu Ado Bayero a fadar Nassarawa
Gwamna Abba ya ba Sanusi II mukami
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba Mai martaba Muhammadu Sanusi II, mukami.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba mai martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.
Sanusi II ya yaba wa Gwamna Abba bisa gagarumin aikin ci gaba da yake aiwatarwa, tare da ba da tabbacin cewa sarakuna za su yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da inganta zaman lafiya a Kano.
Asali: Legit.ng

