Gwamnati Ta Fadi Jiha 1 da Za Ta Iya Tatso Harajin Naira Tiriliyan 1 duk Shekara
- Taiwo Oyedele ya ce jihar Legas kadai za ta iya samun Naira tiriliyan daya duk shekara idan ta inganta tsarin karbar harajin kadarori
- Shugaban kwamitin sake fasalin haraji na shugaban kasa ya tabbatar da cewa gidaje miliyan biyu kacal sun isa su samar da harajin
- Ya kuma kawo wasu abubuwa biyu da idan gwamnati ta yi riko da su, mutane ba za su rika jin tsoron bayar da harajin da ke kansu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Shugaban kwamitin sake fasalin haraji da manufofin kuɗi na shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya yi magana game da damarmakin haraji a jihar Legas.
Taiwo Oyele ya ce Legas tana da damar tatsar kusan Naira tiriliyan 1 a kowace shekara daga harajin kadarori idan har aka bi hanyoyin da suka dace.

Source: Twitter
Jihar Legas za ta iya tatso harajin N1trn
Shugaban kwamitin ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin babban taron tattaunawa kan haraji na shekarar 2026, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
A cewar Oyedele, harajin kadarori yana ɗaya daga cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da ba a damu da su ba, duk kuwa da cewa hanya ce tabbatacciya ga jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya jaddada cewa idan aka samu gidaje miliyan biyu kacal a Legas waɗanda kowannensu darajarsa ta kai Naira miliyan 100, kuma aka saka musu harajin kashi 0.5 cikin ɗari kawai na darajar gidan, jihar za ta samu tiriliyan ɗaya a kowace shekara.
Wannan kuɗi, a cewarsa, za su taimaka ƙwarai wajen sauya fasalin jihar da samar da ababen more rayuwa da al'umma za su ci gaba da amfana na tsawon lokaci.
Samar da bayanai domin karbar haraji
Oyedele ya bayyana cewa nasarar wannan tsari ya dogara ne kacokan kan samun ingantattun bayanai na masu biyan haraji da kuma tantance darajar kadarori.
Ya bayyana cewa bayanai sune ginshiƙin faɗaɗa kason haraji yayin da ya buƙaci jihar Legas da ta nuna jagoranci wajen samar da tsarin doka da zai tafi daidai da zamani don rage tsadar biyan haraji da kuma ƙara wa masu biya kwarin gwiwa.
Ya ce dole ne a samu sahihan bayani kan yawan mutanen da ke aiki da kuma darajar gidajen da suke ciki domin samun adalci, in ji rahoton Sucess FM.

Source: Original
Tasirin karbar harajin kadarori ga al'umma
Ya ƙara da cewa harajin kadarori yana da wahalar kaucewa idan aka tsara shi da kyau, kuma yana bunƙasa ne daidai da bunƙasar birane.
"Idan aka karbi waɗannan kuɗade aka zuba su wajen samar da hanyoyi, ruwan sha, wutar lantarki, da sauran ababen more rayuwa, hakan zai ƙara wa gidajen daraja."
"Wannan kuma zai sa rayuwar al'umma ta inganta, sannan su kuma kadarorin su ci gaba da samar da ƙarin kuɗin shiga da za a sake amfani da su don ci gaban al'umma."
- Taiwo Oyedele.
Oyedele ya yi magana kan dokar haraji
A wani labari, mun ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa ta shiga tsakani kan cece-kuce da aka yi game da dokokin haraji da za su fara aiki daga Janairu, 2026.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa, sun bukaci a dakatar da aiwatar da sababbin dokokin.
Shugaban kwamitin gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya ce masu adawa da dokoki ba su fahimci yadda tsarin yake ba, yana mai cewa dokoki ne za su amfani 'yan kasa.
Asali: Legit.ng


