An Yi Barna: Mummunar Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Jos
- An samu tashin gobara a babbar kasuwar birnin Jos da ke jihar Plateau wadda ta jawo asara ga mutanen da ke neman na abinci
- Gobarar wadda ta tashi a cikin dare ta lakume shagunan 'yan kasuwa kafin daga bisani jami'an hukumar kashe gobara su kawo dauki
- Mahukunta a kasuwar sun bayyana cewa tuni aka fara gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Terminus da ke birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.
Gobarar wadda ta tashi a daren ranar Talata, 23 ga watan Disamban 2025, ta kone kimanin shaguna 25, kamar yadda ’yan kasuwa da jami’an kasuwar suka tabbatar.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce shaidu sun ce jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya da ta jihar Plateau sun kai ɗauki cikin gaggawa.
Jami'an sun yi nasarar shawo kan gobarar kafin ta bazu zuwa sauran sassan kasuwar.
Yaushe gobarar ta tashi?
Sakataren kasuwar, Zakari Sale, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne tsakanin karfe 8:00 zuwa zuwa 9:00 na dare, yana mai cewa barnar da aka yi ba ta kai girman wadda aka saba gani a lokutan baya ba.
"Isowar jami’an kashe gobara da wuri, tare da taimakon wasu masu kishin al’umma, ya hana gobarar yaɗuwa da kona dukiya. Bisa binciken da muka yi, kimanin shaguna 25 ne suka kone.”
- Zakari Sale
A cewar shugabannin kasuwar wannan gobarar ta zo ne watanni bayan wata babbar gobara a watan Afrilun 2025 da ta lalata fiye da shaguna 500, inda aka kiyasta asarar da ta haura Naira biliyan 1.
Kasuwar Terminus ta taɓa fuskantar irin wannan masifa a baya, ciki har da gobarar watan Fabrairu 2001 da ta kona manyan sassan kasuwar tare da jefa ’yan kasuwa da dama cikin matsanancin hali na rashin kuɗi.
Me mahukunta suka ce kan lamarin?
Da take martani kan lamarin na ranar Talata, hukumar kasuwar ta fitar da wata sanarwa a ranar Laraba, inda ta tabbatar da faruwar gobarar, amma ta ce binciken farko bai gano musabbabin tashinta ba.

Source: Original
Hukumar ta ce jami’an tsaro sun killace yankin da abin ya shafa domin kare dukiyar ’yan kasuwa da kuma tabbatar da zaman lafiya kafin dawowar ’yan kasuwa.
Ta bayyana cewa ba a samu asarar rai ba a gobarar tana mai karawa da cewa harkokin kasuwanci sun fara dawowa daidai a kasuwar.
Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar, kuma za a ɗauki matakan kariya domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Gobara ta tashi a kasuwar Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a wata fitacciyar kasuwar kayan gado a jihar Kano.
Mummunar gobarar ta auku ne a kasuwar kayan gado ta Sabuwar Lale da ke Tal’udu, a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.
An yi kira ga gwamnatin jihar Kano da kuma masu hannu da shuni da su tallafa wa ’yan kasuwar da lamarin ya shafa, la’akari da girman asarar da aka yi.
Asali: Legit.ng

