Babban Hafsan Sojoji da Manyan Jami'ai 4 Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Sama a Turkiyya
- An tabbatar da mutuwar babban hafsan sojojin kasar Libya, Janar Mohammed al-Haddad a hatsarin jirgin sama a kasar Turkiyya
- Hafsan sojojin tare da wasu manyan jami'ai hudu da matukan jirgin sama uku sun rasa rayukansu hatsarin a daren jiya Talata
- Gwamnatin Libya da ta Turkiyya sun tabbatar da aukuwar wannan lamari, tare da jimamin rashin wadanda manyan sojoji na Libya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ankara, Turkey - Babban hafsan sojojin Libya da wasu manyan jami’an soja guda hudu sun mutu yayin da jirgin saman da suka ciki ya yi hatsari bayan tashinsa daga birnin Ankara a Turkiyya.
Hukumomin tsaron Ankara na Turkiyya da Tripoli, babban birnin Libya sun tabbatar da aukuwar wannan hatsari da mutuwar manyan hafsoshin sojin.

Source: Getty Images
Ministan cikin gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya ce jami’an tsaro na Turkiyya sun gano tarkacen jirgin Falcon 50 a yankin Haymana kusa da Ankara jim kadan bayan batansa, cewar rahoton Al-Jazeera.
Libya ta tabbatar da mutuwar Al-Haddad
Firaministan Libya, Abdulhamid Dbeibah, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce sun sun yi bakin cikin mutuwar Laftanar Janar Al-Haddad.
“Cikin matukar bakin ciki da damuwa, muna tabbatar da cewa mun samu labarin mutuwar babban hafsan sojojin Libya, Laftanar Janar Mohammed al-Haddad.”
Tun farko dai, Al-Haddad ya je kasar Turkiyya ne somin halartar wani taro da Ministan Tsaron Turkiyya, Yasar Guler da takwaransa na kasar, Selcuk Bayraktaroglu a ranar Talata.
Yadda jirgi ya yi ajalin mutane 8 a Turkiyya
Sai dai bayanai sun nuna cewa bayan kammala wannan taro, babban hafsan sojojin Libya ya hau jirgi da nufin komawa Tripoli, amma ya gamu da hatsarin da ya zama ajalinsa.
Yerlikaya ya bayyana cewa jirgin Haddad ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Esenboga, Ankara da karfe 17:10 agogon GMT, amma kasa da awa guda bayan tashinsa, aka neme shi aka rasa.
"Jirgin ya aika da bukatar saukar gaggawa a kusa da Haymana, kilomita 74 daga Ankara amma ba a sake jin duriyarsa ba daga nan," in ji ministan.
Wani babban jami’in Turkiyya ya ce jirgin ya nemi saukar gaggawa saboda wata matsala da ta shafi wuta mintuna 16 bayan tashinsa.
Jirgin na dauke da fasinjoji takwas, ciki har da Haddad, mambobin tawagarsa guda hudu, da ma’aikatan jirgin guda uku, kuma dukansu sun mutu.

Source: Getty Images
Sauran wadanda suke cikin jirgin sun hada da mai ba Haddad shawara, Mohammed Al-Assawi, Manjo Janar Al-Fitouri Ghraibil, Manjo Janar Mohammed Jumaa, da mai rakiyarsu, Mohammed Al-Mahjoub.
Haddad ya zama babban hafsan sojojin Libya tun watan Agusta 2020, lokacin da tsohon Firaminista Fayez al-Sarraj ya nada shi, kamar yadda tashar Channels ta kawo.
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Turkiyya 20 sun rasu bayan jirgin C-130 da ke dauke da su ya yi hatsari a kasar Georgia.
Gwamnatin kasar Turkiyya ta tabbatar da mutuwar sojojinta guda 20 a hatsarin wanda ya auku a watan Nuwamba, 2025.
Jirgin, wanda ya taso daga Azerbaijan zuwa Turkiyya, ya kife kusa da.iyakar Georgia, inda ya bar tarkacen karafa a cikin wani fili da mai yawan ciyawa.
Asali: Legit.ng

