'An Kusa Gama Gyara Lantarkin Najeriya,' Ministan Makamashi Ya Yi Albishir
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce za a dawo da wutar lantarki cikin awa 24 zuwa 48 bayan 'yar matsalar da aka samu a kwanakin baya
- An danganta matsalar da fashewar bututun iskar gas na Escravos–Lagos da kuma lalata kayayyakin gas a yankin Neja Delta da bata gari suka yi
- Gwamnatin tarayya ta bukaci jama’a su yi hakuri tare da taimakawa wajen kare muhimman kadarorin kasa, musamman wadanda suka shafi wuta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a dawo da wutar lantarki kamar yadda ta ke da bayan raguwar da aka samu.
Bayanin ya fito ne ta bakin hadimin ministan, Bolaji Tunji, wanda ya ce an gudanar da taron hadin gwiwar hukumomi da kamfanonin da ke da alhakin samarwa, rarrabawa da raba wutar lantarki a Najeriya.

Source: Original
Punch ta wallafa cewa ministan ya ce an dauki lamarin da muhimmanci sosai, inda aka umurci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su tabbatar da bin jadawalin gyare-gyaren da aka tsara domin inganta wutar lantarki.
Dalilin raguwar samar da wutar lantarki
Bolaji Tunji ya bayyana cewa raguwar wutar lantarki ta biyo bayan fashewar bututun iskar gas na Escravos–Lagos, lamarin da ayyukan lalata bututun gas suka kara tsananta.
Vanguard ta ce wannan matsala ta hana iskar gas isa ga wasu manyan tashoshin samar da lantarki masu amfani da gas a fadin kasar.
A cewarsa, wannan al’amari ya jawo raguwar samar da wuta a matatar lantarki da dama, wanda hakan ya rage karfin wutar da ke shiga rumbun wuta na kasa, tare da janyo tangarda ga masu amfani da wutar lantarki a gidaje da wuraren kasuwanci.
Ana daf da gyara matsalar wutar Najeriya
A yayin taron, wakilan NISO, kamfanin TCN, kamfanonin samar da lantarki da na rarrabawa sun tabbatar wa ministan cewa ana sa ran kammala gyaran bututun gas da aka lalata cikin awa 24 zuwa 48.
Haka kuma, hukumar NISO ta sanar da jama’a cewa tana sa ido kan ayyukan gyara da kamfanin NGPTC ke gudanarwa, inda ta ce ana daf da kammala aikin kuma ana sa ran dawo da cikakken aiki nan ba da jimawa ba.

Source: Getty Images
NISO ta kara da cewa tashoshin lantarki masu amfani da gas sun fara nuna alamun dawowa aiki, wanda hakan zai taimaka wajen kara adadin wutar da ake samarwa a kasa.
Gwamnatin Najeriya ta bukaci hadin kai
Ministan makamashi ya bayyana cewa ya fahimci irin wahalar da gidaje da ‘yan kasuwa ke fuskanta sakamakon katsewar wuta, musamman ganin karuwar bukatar lantarki a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Adelabu ya bukaci al’umma su kasance masu lura da duk wani abu da ake zargin yana barazana ga kayayyakin lantarki da gas, tare da sanar da jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa kare wadannan kayayyaki nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Tashohin lantarki na barazanar daina aiki
A wani labarin, kun ji cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun fara barazanar daina aiki a lokacin da al'umma suke kokawa.
Wasu kamfanoni a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu sun fitar da sanarwar gargadi ga gwamnatin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanoni na barazanar dauke wuta baki daya ne sakamakon karancin gas da ake fuskanta a halin yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

