APC Ta Fusata bayan Hadimin Gwamna Ya Lakadawa Kansila Dukan Tsiya

APC Ta Fusata bayan Hadimin Gwamna Ya Lakadawa Kansila Dukan Tsiya

  • Jam'iyyar APC ta tsoma baki kan lamarin dukan da wani hadimin gwamna ya yi wa Kansila a jihar Gombe
  • Mai magana da yawun APC na jihar Gombe ya yi Allah wadai da lamarin wanda ya bayyana a matsayin abin da ya sabawa doka
  • Moses Kyari ya bayyana cewa tuni jam'iyyar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin abin da ya hada mutanen biyu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Jam’iyyar APC a jihar Gombe ta yi Allah-wadai kan dukan da hadimin gwamna ya yi wa wani kansila.

Lamarin dai ya faru ne tsakanin wani hadimi ga gwamnan jihar Gombe da ke aiki a Ofishin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Gombe da kuma wani kansila mai ci a ofis, lamarin da ya janyo fushin jama’a sosai.

APC ta yi martani kan dukan kansila a Gombe
Gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce mai magana da yawun APC na jihar Gombe, Moses Kyari, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, jigonta kuma tsohon kwamishina yar bar duniya

An soki dukan kansila a Gombe

Kungiyoyin farar hula da dama, ciki har da Amnesty International da Gombe State Network of Civil Society Organisations, sun yi tir da harin da ake zargin mataimakin gwamnan ya aikata, inda suka nemi a yi adalci tare da korar sa daga aiki.

Bidiyon da ya bazu ya nuna wani daga cikin hadiman gwamnan Gombe da ke ƙarƙashin ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, mai suna Adamu Abdullahi Danko, yana dukan wani kansila mai suna Abdulrahman Abubakar.

Me jam'iyyar APC ta ce kan lamarin?

A cikin sanarwar APC ta bayyana damuwa kan bidiyon, inda ta jaddada cewa jam’iyyar ba ta goyon bayan duk wani nau’in tashin hankali ko aikata abin da ya saɓa doka, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Jam’iyyar APC ta bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali kuma wanda bai dace da kima, ladabi da al’adun dimokuraɗiyya na APC ba.

Moses Kyari ya ce jam’iyyar ta kaddamar da cikakken bincike na cikin gida kan lamarin, tare da kiran mutanen da abin ya shafa domin gano musabbabin rikicin, don kare mutuncinta da kuma hana sake faruwar irin wannan lamari.

Kara karanta wannan

An lakaɗawa Kansila duka kan zargin ba shi kuɗi ya mari na kusa da Gwamna

Kakakin jam’iyyar ya jaddada cewa abin da aka gani a bidiyon an aikata shi ne bisa ra’ayin mutum ɗaya, ba tare da umarni, amincewa ko izini daga jam’iyyar ko wata hukuma ta gwamnati ba.

APC ba ta yarda da daukar doka a hannu ba

Ya kara da cewa ɗaukar doka a hannu ba abin yarda ba ne kuma ba za a lamunta da shi a kowane hali ba.

APC ta ji haushin dukan kansila a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

APC ta kuma yaba wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Alhaji Abubakar Inuwa Kari, bisa hanzarin dakatar da Adamu Danko, daga aiki har sai an kammala bincike.

Jam’iyyar ta tabbatar wa jama’a cewa binciken zai kasance cikin gaskiya tare da bin kundin tsarin APC.

Moses Kyari ya kara da cewa binciken zai duba dukkan muhimman bayanai da suka shafi lamarin, ciki har da yanayin da ya kai ga faruwar rikicin da kuma nazarin wani sakon murya da ake zargin ya tayar da rikicin.

APC ta shirya tarbar Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta shirya tarbar gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, zuwa cikinta.

Jam'iyyar APC za ta gudanar da babban taro domin yin maraba da Gwamna Mutfwang wanda ya sauya sheka daga PDP.

Hakazalika, APC ta yaba da sauya shekar gwamnan wadda ta bayyana a matsayin abin da zai kara karfafa ta a jihar Plateau.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng