Rawani Ya Fadi: Kotu Ta Yanke Wa Basarake da Wani Mutum 1 Hukuncin Kisa a Gombe
- Kotu ta kama basarake da wani mutum daya da laifin kisan kai a jihar Gombe, ta yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Alkalin da ya jagoranci shari'ar, Abdulsalam Mohammad, ya wanke mutum uku da aka gurfanar da su tare saboda rashin hujjoji
- An dai kama tare da gurfanar da hakimin Bangunji, Sulei Yerima bisa jikkata wani mutumi, wanda raunin ya zama ajalinsa a Gombe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba takwas ta samu Hakimin Gundumar Bangunji, Sulei Yerima, da kuma abokinsa, Shedrack Aliyu Kwan, da hannu a aikata kisan kai.
Bisa haka, kotun mai zama a cikin birnin Gombe ta yanke wa basaraken da wanda suka aikata laifin tare hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Source: Original
Daily Trust ta ce Mai shari’a Abdulsalam Mohammad, wanda ya yanke hukuncin, ya kuma wanke mutane uku l, Hamisu Ingila, Shanono Sarkin Pawa da Joseph Sarkin Noma saboda babu hujjar da ta nuna suna da hannu a kisan kan.
Yadda hakimi da abokinsa suka yi kisa
Tun farko an gurfanar da su ne kan tuhume-tuhumen makarƙashiya, taimakawa aikata laifi, ji wa mutum mummunar rauni da kuma kisan kai, wanda ya saba wa tanadin dokokin Penal Code.
A cewar masu gabatar da ƙara, lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Agusta, 2017, a ƙauyen Biwula kusa da Bangunji a ƙaramar hukumar Shongom.
Masu karar sun tabbatar wa kotu cewa waɗanda ake tuhuma da haɗa kai suka kai wa Shu’aibu Sale Galadima hari, suka jikkata shi, har raunin ya yi sanadin mutuwarsa saboda kawai ya tsokani daya daga cikinsu.
An gabatar da hujjoji a kotun Gombe
A yayin shari’ar, ɓangaren gwamnati ya gabatar da shaidu 10 a farko, tare da karin wasu daga baya yayin da lauyoyin wadanda ake kara suka gabatar da shaidu guda shida.
Dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta aikata laifin tun a farko-farkon shari'ar, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Bayan nazari, Mai shari’a Mohammad ya ce kotu ta gamsu tare da tabbatar da laifin Sulei Yerima da Shedrack Aliyu Kwan, yana mai bayyana hujjojin da aka gabatar a kansu a matsayin masu ƙarfi da gamsarwa.

Source: Getty Images
Sai dai ya ce hujjojin da suka shafi sauran mutum uku ba su isa su gamsar da kotu cewa suna da hannu laifin ba, saboda an ambaci sunayensu ne kawai ba tare da tabbataccen shaida ba.
A ƙarshe, kotu ta yanke wa hakimin, Sulei Yerima da Shedrack Aliyu Kwan hukuncin kisa ta hanyar rataya, kamar yadda doka ta tanada.
DSS ta gurfanar da Obadaki kan kisan mutane
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar DSS ta maka Abdulmalik Abdulazeez Obadaki a gaban kotu bisa zargin hannu a harin da aka kai wata coci a jihar Kogi
Ana zargin Obadaki da jagorantar harin da aka kai wa cocin Deeper Life Bible Church da ke Otite kusa da Okene a Kogi a shekarar 2012, inda aka kashe mutane 19.
DSS ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja , inda aka tuhume shi da aikata laifuffuka shida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


