'Yan Bindiga Sun Lafta Kudin Fansa bayan Sace Masu zuwa Mauludi a Plateau

'Yan Bindiga Sun Lafta Kudin Fansa bayan Sace Masu zuwa Mauludi a Plateau

  • 'Yan bindiga sun yi wa masu zuwa wajen taron Mauludi kwanton bauna a jihar Plateau, tare da tafiya da su cikin daji
  • Bayan sace mutanen, 'yan bindigan sun kira 'yan uwansu inda suka bukaci a ba su miliyoyi a matsayin kudin fansa
  • Sai dai, 'yan uwan sun koka da cewa su talakawa ne ba za su iya biyan makudan kudin da 'yan bindigan suka nema

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - ’Yan bindigan da ake zargin sun yi garkuwa da matafiya 28 a kauyen Zak, gundumar Bashar, a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau, sun bukaci a ba su kudin fansa.

'Yan bindigan sun tuntubi iyalan waɗanda aka sace tare da neman kudin fansa na Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum.

'Yan bindiga sun bukaci kudin fansa kan mutanen da suka sace a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Ibrahim Musa, ya shaida wa jaridar Daily Trust hakan a ranar Talata, 23 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya masu zuwa Mauludi a Plateau

'Yan bindiga sun sace masu zuwa Mauludi

An sace matafiyan ne a daren Lahadi yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Sabon Layi domin halartar bikin Mauludi.

Rahotanni sun ce ’yan bindigan sun yi kwanton bauna ga motar da ke ɗauke da su, suka sace dukkan fasinjojin, sannan suka bar motar a wurin.

Nawa 'yan bindiga suka nema a biya su?

Ibrahim Musa ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan, inda suka dage sai an biya Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum kafin a sake su.

"Yan bindigan sun kira ni a daren jiya, suka ce dole a biya Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum, ba tare da la’akari da shekaru ko jinsin mutum ba. Amma sun tabbatar mana cewa mutanenmu suna lafiya kuma babu abin da zai same su.”

- Ibrahim Musa

Ibrahim Musa ya bayyana cewa ya roki ’yan bindigan, yana sanar da su cewa iyalan talakawa ne kuma ba za su iya biyan irin wannan kuɗi ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi aika aika bayan kai wani harin ta'addanci a Zamfara

"Na gaya musu mu mutanen kauye ne, ba mu da irin wannan kuɗi. Rayuwa ma tana da wahala a nan. Yawancin waɗanda aka sace matasa ne, kuma iyayensu ba za su iya tara irin wannan adadi ba. Don haka na roke su da su ji tausayi.”

- Ibrahim Musa

'Yan bindiga sun bukaci a ba su kudin fansa a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun tabbatar da lamarin

Tun a ranar Litinin, Rundunar ’yan sandan jihar Plateau ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara bincike kan lamarin.

A halin da ake ciki, mazauna yankin sun yi kira da a kara tsaurara matakan tsaro domin dakile yawaitar sace-sacen mutane, ayyukan ’yan bindiga da satar shanu a karamar hukumar Wase.

'Yan bindiga sun kashe basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani mummunan hari a jihar Kwara.

Harin ya yi sanadin mutuwar wani basarake da aka bayyana sunansa da Dennis, yayin da aka sace wani tsohon jami’in Kwastam mai suna Emmanuel Owolabi.

Majiyoyi sun bayyana cewa mutanen yankin sun rika gudu domin tsira da rayukansu yayin harin da 'yan bindigan suka kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng