Aisha Buhari Ta Fallasa Yadda aka So Korar ta, ’Ya’yanta daga Fadar Shugaban Kasa
- Tsohuwar Uwargidan shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayyana yadda wasu masu karfi a Aso Villa suka yi yunkurin tursasa ta da ’ya’yanta fita daga fadar shugaban kasa
- A bayanin da ta yi, ta ce wasu mutane sun yi amfani da kaunar da Muhammadu Buhari ke yi ga ’yan uwansa da tsofaffin abokansa wajen shafar tafiyar da gwamnatinsa
- Hajiya Aisha Buhari ta gargadi shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya maimaita kuskuren rike jami’ai marasa aiki tukuru kamar yadda ya faru a mulkin mijinta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi bayani dalla-dalla kan irin matsin lamba da ta fuskanta daga wasu manyan mutane da ke zaune a Aso Villa a lokacin mulkin mijinta, Muhammadu Buhari.
A cewarta, wasu daga cikin wadannan mutane sun hada da iyalansu, matansu da jikokinsu, inda suka nemi mamaye fadar shugaban kasa tare da kokarin korar ta da ’ya’yanta daga ciki.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa wadannan bayanai sun fito ne a cikin littafin tarihin tsohon shugaban kasa mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr. Charles Omole ya rubuta.
Maganar korar Aisha Buhari a Aso Villa
Littafin ya bayyana cewa Aisha Buhari ta bayyana Aso Villa a matsayin wani irin muhalli da ke cike da wani salon siyasa, inda makirci ke tasiri.
Ta ce tun daga shekarar 2017, wasu ’yan uwa da makusanta suka fara cika Aso Villa, suna kokarin mallake ko ina a ciki.
A cewarta, wadannan mutane sun nemi su zama masu iko a ofishin mijinta tare da kuma nuna tasiri a cikin gidanta, lamarin da ta ce ba za ta amince da shi ba.
Ta jaddada cewa fadar shugaban kasa gidanta ne, kuma ba za ta yarda a raba ikon mijinta da ikon rayuwarta ta gida ba.
Aisha Buhari ta ce an juya Shugaban kasa
Aisha Buhari ta yi nuni da cewa kaunar da Buhari ke yi wa ’yan uwansa da tsofaffin abokansa ta sanya shi cikin hadarin yaudarar wasu.
Littafin ya ce wasu mutane sun fahimci wannan rauni, suka yi amfani da shi wajen cimma muradunsu, wanda hakan ya jawo cikas ga manyan manufofin gwamnatin Buhari.

Source: Facebook
Ta bayyana cewa wasu ’yan uwa da ba su da mukami a gwamnati sun fara tsoma baki wajen shigar mutane Aso Villa, yayin da wasu tsofaffin abokan Buhari da suka sha wahala tare da shi a lokacin adawa suka fara fuskantar kalubale.
Dalilin fitowarta fili da gargadi ga Tinubu
Littafin ya ce Aisha Buhari ta fara kai wadannan koke-koke a boye, amma ganin babu wani canji, sai ta fito fili ta bayyana damuwarta.
Ta yi imanin cewa tsufa, tsoron yadda jama’a za su kalli gwamnati, da kuma tausayi ga wasu jami’ai sun hana Buhari daukar mataki kan wadanda ba sa aiki yadda ya kamata.
Ta yi gargadi ga Bola Ahmed Tinubu da kada ya sake wannan kuskure, ta ce dole ne shugaba ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da aiki nagari domin cimma muradun al’umma.
Maganar sake auren Aisha Buhari
A wani labarin, kun ji cewa matar tsohon shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta yi magana kan sake aure bayan rasuwarsa.
A bayanin da ta yi, Aisha Buhari ta bayyana cewa ba za ta sake wani aure ba, za ta zauna ta cigaba da kula da yara da jikoki.
Aisha Buhari ta kara da cewa tana so ta taso cikin jikokinta, su samu lokaci su zauna tare da ita kafin rai ya yi halinsa a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


