Sheikh Jingir Ya Gargadi Tinubu kan Dokar Haraji da za Ta Fara Aiki a 2026
- Muhammad Sani Yahaya Jingir ya nemi gwamnati ta zauna a sake duba dokar harajin Bola Ahmed Tinubu idan har za ta jawo wa jama’a wahala
- Sheikh Jingir, duk da kasancewarsa mai goyon bayan Shugaba Tinubu, ya yi gargadi cewa bai dace a ɗaura wa ‘yan kasa abin da ya fi karfinsu ba
- Ce-ce-ku-ce kan dokar harajin ya ƙara ƙarfi, Audu Bulama Bukarti, ya yi zargin an yi kutse da canji a dokar bayan majalisar tarayya ta amince da ita
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban malaman kungiyar Izala na kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi magana kan sabuwar dokar haraji da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke shirin aiwatarwa.
Sheikh Jingir, wanda aka fi sani da nuna goyon baya ga shugaba Tinubu a lokuta da dama, ya bayyana cewa bai kamata a daura wa jama'a abin da ya fi karfinsu ba.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Sheikh Jingir ya yi ne a wani bidiyo da wani dan agajin Izala, Ibrahim Maina Muhammad ya wallafa a Facebook.
Gargadin Sani Jingir ga Bola Tinubu kan haraji
A jawabin da ya yi, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kira kai tsaye ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba dokar harajin idan har gaskiya ne za ta cutar da bayin Allah.
Sheikh Jingir ya yi tsokaci kan rikicin da ke tsakanin gwamnati da ‘yan jaridu game da dokar, inda ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne tasirin dokar a kan talakawan kasa.
A cewarsa, idan haraji zai jefa jama’a cikin ƙuncin rayuwa, to bai kamata shugaban kasa ya shiga wani hali da zai yi wahala ya fita daga ciki ba.
A cewarsa:
"Ahmad Bola Tinubu ina hada ka da Allah, wannan abin da ya shiga tsakaninku da 'yan jaridu, mu ba mu san kan labaransu, ba mu san na gwamnati ba.

Kara karanta wannan
Tinubu bai ce uffan ba, Majalisa za ta binciki zargin canza dokar haraji ta bayan fage
"Ku je ku zauna a duba, indai gaskiya haraji zai cuce mu, to Ahmad Bola Tinubu kar ka shiga wajen da ba za ka iya fita ba.
"Don bayi na Allah ne. Kar ka daura mana abin da ya fi karfinmu. Da ba kai ne shugaban kasar ba, wallahi watarana ma ba kai ba ne."
Ce-ce-ku-ce kan sahihancin dokar haraji
Dokar harajin Tinubu ta janyo muhawara mai zafi, lauya Audu Bulama Bukarti, ya bayyana damuwarsa kan zargin cewa an canja dokar bayan majalisar tarayya ta amince da ita.
Lauyan ya wallafa a Facebook cewa yawancin ‘yan Najeriya na da dalilin kiran a dakatar da aiwatar da dokar kuma matsalar ta wuce batun lokaci ko tsari na haraji kawai.

Source: Facebook
Bukarti ya ce idan har gaskiya ne an yi wa dokar da majalisa ta amince da ita gyara a asirce kafin a wallafa ta, to hakan hari ne kai tsaye ga tsarin dimokuradiyyar kundin tsarin mulki.
Martanin gwamnati kan dokar harajin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi magana yayin da ake zargin sauya dokokin haraji ta bayan fage.
A makon da ya wuce ne wani dan majalisar wakilai ya yi zargin cewa an sauya wasu abubuwan da suka amince da su.
Shugaban kwamitin harajin ya bayyana cewa babu abin da suka canja a ciki, ya ce suna aiki ne da abin da aka ba su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

