Kirsimeti: Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Al'ummar Kiristoci a Borno

Kirsimeti: Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Al'ummar Kiristoci a Borno

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba kayan abinci masu muhimmanci ga al'ummar Kirista.

Gwamna Zulum ya raba kayayyakin ne ga zawarawa da kuma marasa galihu daga al’ummar Kirista, domin shirye-shiryen bikin Kirsimeti mai zuwa.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa Gwamna Zulum ya jagoranci rabon kayan tallafin a ranar Litinin, 22 ga watan Disamban 2025.

Kowanne daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, sama da mutane 6,000, ciki har da ’yan gudun hijira 1,605, ya samu buhun shinkafa guda ɗaya, kwali ɗaya na taliya da kuma galan ɗaya na man girki.

A cewar Zulum, wannan rabon daga cikin tallafin da yake bayarwa a kowace shekara ga Kiristoci domin rage musu dawainiya tare da tabbatar da cewa sun yi bikin Kirsimeti cikin farin ciki da mutunci.

Gwamnan ya kuma amince da sufuri kyauta ga Kiristocin da ba ’yan asalin Borno ba, domin su tafi zuwa garuruwansu na asali yayin bukukuwan.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Zulum ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai da bunkasa tattalin arziki tare a tsakanin dukkan al’ummar jihar Borno, ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabila ba.

"Fatan da na ke da shi a zuciyata shi ne dangantakar da ta daɗe tsakanin Musulmi da Kiristoci a jihar Borno ta ci gaba da dorewa."

"Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki, cikin rahamarsa marar iyaka, Ya albarkaci al’ummominmu, Ya kuma tabbatar da zaman lafiya da jituwa tsakanin addinan biyu.”

"Koyarwar Musulunci ta fayyace cewa Musulmi suna buƙatar zaman tare cikin lumana da waɗanda ba Musulmi ba, kamar yadda Alƙur’ani ya koyar, kuma na yi imanin cewa akwai hakan a cikin littafin Kirista”

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a jihar Borno, Rabaran John Bogna Bakeni, wanda ya tarbi gwamnan, ya nuna godiya mai yawa bisa ci gaba da nuna tausayi da tallafin da yake bayarwa.

"Muna miƙa godiyarmu gare ka, Mai Girma Gwamna. Wannan abu yana da matukar muhimmanci a gare mu, al’ummar Kirista a jihar Borno."

- Rabaran John Bogna Bakeni

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng