Ana Wata ga Wata: An Hango Jirgin Leken Asirin Amurka Yana Shawagi a Najeriya
- Tun daga Nuwamba, 2025 ne aka rahoto cewa wasu jiragen leken asirin kasar Amurka na yin shawagi a sararin samaniyar Najeriya
- Rahotanni sun danganta hakan da barazanar daukar matakin sojoji da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi a kwanakin baya
- Jiragen na tattara bayanai kan Boko Haram da ISWAP tare da bin sawun wasu masu garkuwa da mutane don sanin maboyarsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta fara tura jiragen leken asiri a manyan sassan Najeriya tun daga karshen watan Nuwamba, 2025.
Rahoton na musamman da aka fitar a ranar Litinin, bisa bayanan bin diddigin jirage da kuma majiyoyin gwamnatin Amurka, ya ce ba a iya tabbatar da ainihin manufar ayyukan wadannan jirage ba.

Source: Twitter
Kamfanin jaridar Rauters ya rahoto cewa wannan mataki na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Najeriya a watan Nuwamba, 2025.
A lokacin, ya yi baraanar daukar matakin soji a Najeriya saboda abin da ya bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen dakile hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kirista.
Haka kuma, ayyukan leken asirin sun zo ne bayan sace wani matukin jirgin Amurka da ke aiki da wata kungiyar yada addini a kasar Nijar a watannin baya.
Bayanan bin diddigin jirage na watan Disamba, 2025 sun nuna cewa jiragen da ke gudanar da aikin yawanci, suna tashi daga Ghana, suna shawagi a sararin samaniyar Najeriya, sannan su koma Accra, babban birnin Ghana.
An gano cewa kamfanin da ke sarrafa jiragen shi ne Tenax Aerospace, wani kamfani da ke jihar Mississippi a Amurka, wanda ke samar da jiragen ayyuka na musamman kuma ke aiki kafada da kafada da sojojin Amurka.
Sai dai kamfanin bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Ghana: Cibiyar aikin sojin Amurka
Shugaban tawagar Afirka da ke kula da muhimman ayyuka a cibiyar Amurka (AEI), Liam Karr, wanda ya yi nazari kan bayanan jiragen, ya ce alamu na nuna ana gudanar da aikin ne daga Accra.
A cewar Liam Karr, Accra sananniya ce a matsayin cibiyar dabaru da kayayyakin aiki ta sojojin Amurka a Afirka, in ji rahoton Punch.
Liam Karr ya ce wannan na iya nuna cewa Amurka na sake gina karfin leken asirinta a yankin, musamman bayan da Nijar ta kori sojojin Amurka daga wani muhimmin sansanin jiragen sama a hamada, tare da karkata ga Rasha domin taimakon tsaro.

Source: Twitter
Mayar da hankali kan Boko Haram da ISWAP
Wani tsohon jami’in Amurka ya bayyana cewa jirgin na daga cikin wasu kadarorin tsaro da gwamnatin Trump ta mayar da su Ghana a watan Nuwamba.
Ya ce ayyukan jirgin sun hada da; bin sawun matukin jirgin Amurka da aka sace, tattara bayanai kan kungiyoyin ‘yan ta’adda a Najeriya, ciki har da Boko Haram da ISWAP.
Wani jami’in gwamnati na yanzu ya tabbatar da cewa jirgin na shawagi a sararin samaniyar Najeriya, amma ya ki bayar da cikakken bayani saboda dalilan diflomasiyya.
Najeriya da Amurka sun yi sasanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa rikicin diflomasiyya da ya taso tsakaninta da Amurka ya lafa matuka bayan doguwar tattaunawa.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai na karshen shekara da aka gudanar a Abuja.
Ministan ya ce rikicin ya biyo bayan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, inda ya zargi Najeriya da yi wa Kiristoci kisan gilla tare da yin barazanar daukar matakin soji.
Asali: Legit.ng


