Tinubu Ya Sa Lokacin da Jakadu Za Su Fara Aiki bayan Amincewar Majalisa
- Majalisar dattawa ta kammala aikin tantancewa tare da amincewa da nadin sababbin jakadun da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi
- Biyo bayan hakan, gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin da sababbin jakadun Najeriya za su fara aiki a kasashen duniyan da aka tura su
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya bayyana cewa sababbin jakadun za su fara aiki ne a shekarar 2026
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sababbin jakadun Najeriya da aka naɗa za su kama aiki.
Mohammed Idris ya ce sababbin jakadun za su fara aiki a kasashen da aka tura su a shekarar 2026, bayan majalisar dattawa ta tantance su tare da tabbatar da su.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 22 ga watan Disamban 2025 yayin da yake yi wa ’yan jarida bayani a taron manema labarai na karshen shekara da aka gudanar a Abuja.
Majalisar dattawa ta amince da nadin jakadu
A makon da ya gabata, majalisar dattawa ta tabbatar da mutane 64 da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin jakadu, ciki har da tsohon Ministan sufurin jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da kuma tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Reno Omokri.
An tabbatar da naɗin ne bayan majalisar dattawa ta duba tare da amincewa da rahoton kwamitin harkokin kasashen waje.
Kwamitin ya ce an tantance dukkan waɗanda aka naɗa tare da tabbatar da cewa sun cancanci rike mukaman.
Yaushe jakadun Najeriya za su fara aiki
A cewar ministan, tura jakadun zai kara karfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe, jaridar TheCable ta dauko labarin.
“A shekarar 2026, sababbin jakadun da aka naɗa za su kama aiki a kasashen da aka tura su. Hakika, majalisar dattawa ta riga ta tantance su tare da tabbatar da naɗinsu.”
- Mohammed Idris
Ministan ya kara da cewa an yi waɗannan naɗe-naɗen ne sakamakon korafe-korafe da kiraye-kirayen jama’a na a tura jakadu zuwa ofisoshinsu, inda ya ce shugaban kasa ya dauki mataki domin magance hakan.
Tinubu ya saurari koke-koke kan jakadu
"A baya, an sha jin koke-koke da matsin lamba na a tura jakadu su koma wuraren aikinsu. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika wannan bukata.”
- Mohammed Idris

Source: Twitter
Mohammed Idris ya kuma bayyana cewa duk da cewa an kammala wasu matakai na aikin tura jakadun, sauran matakan za a kammala su ne a shekara mai zuwa.
"Sauran matakan da suka rage za a kammala su ne a 2026.”
- Mohammed Idris
Ministan ya jaddada cewa tura jakadun zai ƙara ƙarfafa hulɗar diflomasiyyar Najeriya a fannoni daban-daban tare da cigaba da kare muradun kasa a cikin al’ummar duniya.
Bola Tinubu ya nada jakadun kasashen waje
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zabi jakadun da za su wakilci Najeriya a kasashen waje.
Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawa sunayen sababbin jakadu 32 domin tantancewa da tabbatarwa.
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, na daga cikin mutanen da aka zabo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

