Dangote Ya Taso Wani Fitaccen 'Dan Kasuwa a Kaduna, Ya Yi Barazanar Maka Shi a Kotu
- Hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya nuna bacin ransa kan zarge-zargen da wani dan kasuwa a Kaduna ya masa
- Dangote ya ba dan kasuwar, Kailani Mohammed wa'adin mako guda ya fito bainar jama'a ya nemi afuwarsa kuma ya karyata kansa
- Ya ce idan kuma ba haka ba, zai maka shi a gaban kotu sannan ya nemi diyya mai tsanani kan zargin bata masa suna da kazafi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Group, Aliko Dangote, ya taso wani sanannen dan kasuwa a jihar Kaduna, Kailani Mohammed bisa zargin bata masa suna.
Dangote ya bai wa ɗan kasuwar wa’adin kwana bakwai domin ya janye kalamansa tare da ba da haƙuri a bainar jama’a, ko kuma ya maka shi a kotu kuma ya nemi diyyar Naira biliyan 100.

Source: Getty Images
Jaridar Bussiness Day ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne cikin wata wasika mai kwanan wata Asabar, 20 ga Disamba, 2025, wadda lauyan Dangote, Ogwu James Onoja, ya aike wa Kailani Mohammed.
Abin da dan kasuwan ya yi wa Dangote
A cikin wasikar, Dangote ya zargi Mohammed da yin kalaman ɓatanci, ƙarya da bata suna a kansa da kuma harkokinsa na kasuwanci yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Trust TV a ranar 17 ga Disamba, 2025.
An ce Kailani ya yi kalaman ne yayin da yake martani kan ƙorafin da Dangote ya shigar a Hukumar ICPC, dangane da Farouk Ahmed, tsohon Manajan Darakta na Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA).
A yayin hirar, Kailani ya nuna shakku kan hanyar da Dangote ya tara dukiya, inda ya kuma zarge shi da yin abin da ya kira “kasuwanci mara tsafta” a Fatakwal tun a shekarar 1980.
Dangote ya musanta zargin Kailani
Lauyoyin Dangote sun bayyana kalaman dan kasuwar a matsayin marasa tushe, mugunta da kuma ɓatanci.
Sun kara da cewa kalaman sun nuna Dangote a matsayin mutum mai cin hanci, mai danniya ta kasuwanci, sannan kuma mutumin banza ta fuskar ɗabi’a.
Dangote ya musanta zargin tare da tabbatar da cewa bai taɓa yin wani kasuwanci a Fatakwal ba, ko a 1980 ko a wani lokaci daban, yana mai cewa zargin ƙagagge ne tsantsa kuma ba shi da tushe.
Sharuddan da Dangote ya gindaya
Don haka, Dangote ya nemi dan kasuwan ya fito a wannan gidan talabijin na Trust TV, ya bayyana hujjar da ta sa ya yi irin waɗannan kalamai, ya janye su gaba ɗaya, tare da bayar da haƙuri ba tare da wani sharadi ba.
Haka kuma, attajirin na neman diya ta Naira biliyan 100 kan abin da ya kira bata suna, tare da rubutaccen alƙawari daga Mohammed cewa ba zai ƙara yin irin waɗannan kalamai ba a nan gaba.

Kara karanta wannan
Abin da ya sa ake ganin ya kamata a daure kusan duka ministocin Buhari a gidan yari
Wasikar ta yi gargaɗin cewa idan Kailani Mohammed ya kasa cika waɗannan buƙatu cikin kwana bakwai da karɓar wasikar, Dangote zai ɗauki matakan shari’a.

Source: Getty Images
Hukumar ICPC ta gayyaci Aliko Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar ICPC ta gayyaci shugaban Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote game da korafin da ya shigar kan tsohon shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed.
Hukumar ICPC ta aika wa Dangote da wasikar gayyatar ne domin ya ba da ƙarin bayani dangane korafin da ya kai gabanta kan Farouk Ahmed.
Majiyoyi sun bayyana cewa ICPC ta bukaci Dangote ya miƙa dukkan hujjoji da takardun shaidar da ke goyon bayan korafinsa ga hukumar yaki da cin hanci.
Asali: Legit.ng

