Gwamnati Ta Yi Bayani game da Dokar Haraji da Za Ta Fara Aiki a Sabuwar Shekara
- Fadar shugaban ƙasa ta shiga tsakani kan cece-kuce da aka yi game da dokokin haraji da za su fara aiki daga 1 ga watan Janairu, 2026
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi, tsohon dan takarar Shugaban Kasa, sun bukaci a dakatar da aiwatar da dokokin
- Shugaban Kwamitin Tsare-Tsaren Kudi da Dokokin Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya yi karin bayani game da dokokin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fadar shugaban ƙasa ta bayyana matsayarta kan dokokin haraji da aka tsara su fara aiki daga farkon shekara mai zuwa, bayan cece-kuce da suka taso a tsakanin jama’a da ’yan siyasa.
Wannan batu ya biyo bayan kiran tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ’dan takarar shugaban ƙasa na 2023 na LP, Peter Obi na dakartar da aiwatar da dokar.

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa cewa haka kuma, wani ɗan majalisa, Hon. Abdulsamad Dasuki, ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira sabani tsakanin dokokin da Majalisa ta amince da su da kuma wadanda aka buga a jaridar gwamnati.
Gwamnatin tarayya ta yi magana kan dokar haraji
Rahoton ya ce Dasuki ya ce an koka tare da take hakkinsa a matsayin ɗan majalisa saboda abun da aka buga a matsayin dokar haraji bai nuna abin da aka tattauna a majalisa.
Taiwo Oyedele, shugaban Kwamitin Tsare-Tsaren Kudi da Dokokin Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce rahotannin da ke yawo a kafofin yada labarai ba su da tushe.
Oyedele ya ce ba su da kwafin dokokin da aka amince da su a majalisa domin duba, kuma abin da aka mika wa Shugaban ƙasa don sanya hannu shi ne kawai suke da shi.
Yadda Tinubu ya sa hannu kan dokar haraji

Kara karanta wannan
Tinubu bai ce uffan ba, Majalisa za ta binciki zargin canza dokar haraji ta bayan fage
Ya kuma jaddada cewa abin da ya bayyana a kafofin yada labarai ba daga kwamitin Majalisar wakilai ba ne, kuma ya kamata a bar su su gudanar da bincike.

Source: Facebook
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokokin haraji guda huɗu, wanda gwamnati ta bayyana a matsayin babban sauyi a tsarin haraji na ƙasar cikin shekaru da dama.
Gwamnatin tarayya ta ce sauye-sauyen na nufin sauƙaƙe biyan haraji, faɗaɗa tushen haraji, kawar da maimaita haraji, da kuma zamanantar da tattara haraji a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
Majalisa ta fara bincike kan dokar haraji
A baya, mun wallafa cewa biyo bayan wallafa sababbin dokokin haraji da gwamnatin tarayya ta yi, wasu ’yan majalisa sun gano cewa akwai sabani tsakanin abin da Majalisar Tarayya ta amince da shi da aka buga.
Hon. AbdulSamad Dasuki na PDP daga Sakkwato ya bayyana wannan batu a zauren majalisa, inda ya ce dokokin da aka wallafa ba su yi daidai da abin da ‘yan majalisa suka tattauna da amincewa da shi ba.
Ya bukaci Majalisar Wakilai ta dauki wannan batu da muhimmanci, kuma tuni Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya kafa kwamitin wucin gadi na mutum bakwai domin bincike kan sabanin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
