Bayanai na Kara Fitowa a kan Yadda Gwamnati Ta Ceto Daliban Neja
- Dalibai da ma’aikatan makarantar St Mary’s Catholic da ke Papiri a Jihar Neja sun samu ’yancinsu bayan shafe kusan wata guda a hannun masu garkuwa
- An sako mutane 130 ne a kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, inda aka kai su Minna ta wasu garuruwa bayan sun shafe makonni a wajen 'yan ta'adda
- Duk da ikirarin gwamnati cewa an saki kowa, har yanzu akwai sabanin alkaluma kan ko an ceto dukkannin daliban da malaman da aka sace tun a farko
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – An samu karin bayani kan dalibai da ma’aikatan makarantar St Mary’s Catholic, Papiri, da ke Jihar Neja, wadanda suka samu ’yanci a ranar Lahadi.
Dalibai da malaman sun samu shakar 'yanci ne kusan wata guda bayan da aka sace su daga dakunan kwanan su a ranar 21 ga Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa an sako mutanen ne a wani wuri kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Yadda aka ceto daliban makaranta a Neja
Daily Post ta wallafa cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar da sakin mutane 130 da suka hada da dalibai da ma’aikata. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin.
Rahoton ya kara da cewa bayan karban daliban, an yi jigilar su ta garuruwan Wawa, Mokwa da Bida kafin a kai su Minna, babban birnin jihar.
Wasiu Abiodun ya ce wadanda aka sako sun hada da dalibai da ma’aikatan makarantar. Ya kara da cewa za a sanar da jama’a karin bayani idan an samu wata nasara.
Haka kuma, kakakin fadar shugaban kasa, Sunday Dare, ya sanar bayyana cewa babu ko mutum guda da ya rage a hannun masu garkuwa.
An samu sabani game da sakin daliban
Sai dai duk da wadannan bayanai, har yanzu ana ci gaba da samun sabani kan adadin mutanen da aka sace da kuma wadanda aka sako.
A baya, shugabannin makarantar da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) sun ce adadin mutanen da suka rage a hannun masu garkuwa ya kai 165 bayan da aka saki mutane 100 a ranar 7 ga Disamba.
Bisa wannan lissafi, ana fargabar cewa kimanin mutane 35 na iya kasancewa ba a gano halin da suke ciki ba, lamarin da ke kara tayar da hankula.

Source: Facebook
Sakin mutanen ya zo ne bayan alkawarin da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi wa shugabannin makarantar cewa za a saki sauran mutanen kafin Kirsimeti.
A harin da aka kai makarantar da sassafe a ranar 21 ga Nuwamba, 2025 an kiyasta cewa dalibai da ma’aikata kusan 265 aka sace, bayan da kimanin mutane 50 suka samu damar tserewa.
An ceto daliban da aka dauke a Neja
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an samu nasarar ceto dukkannin ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, a Jihar Neja da aka yi garkuwa da su.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana ceto mutanen a matsayin babbar nasara da ta kawo sauƙi ga ƙasa baki daya.
Sanarwar ta ce sakin ɗalibai 130 na ƙarshe ya kawo ƙarshen wani mummunan lamari da ya jefa iyaye, malamai da al’ummar yankin cikin tsananin fargaba tun bayan faruwar kwashe yaran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


