Saukin da Dangote Ya Yi Ya Jawo 'Yan Kasuwa Fara Rage Farashin Fetur a Najeriya

Saukin da Dangote Ya Yi Ya Jawo 'Yan Kasuwa Fara Rage Farashin Fetur a Najeriya

  • Rage farashin mai a matatar Dangote ya jawo cunkoson masu saye a gidajen mai da ke sayarwa a kasa da N800, yayin da masu tsadar farashi ke rasa abokan hulda
  • Matsin lamba daga masu mota ya tilasta wa wasu gidajen mai rage farashi har kusan N100 kan lita, duk da hakan na jawo asara ga diloli da masu shigo da mai
  • Kamfanoni da dama, ciki har da NNPC, sun fara daidaita farashi domin ci gaba da gogayya a kasuwa, yayin da rikicin ke kara zafi a bangarorin man fetur a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Takaddama kan farashin fetur a Najeriya ta shiga sabon salo bayan da gidajen man MRS a jihohin Lagos da Ogun suka fara sayar da mai da matatar Dangote ta samar a kan N739.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Rahoto ya nuna cewa matakin ya jawo sauya yanayin sayen mai, inda direbobi suka fara kauracewa gidajen mai da ke sayarwa da tsada.

Wasu mutane a layin gidan mai
Mutane na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa sauyin ya tilasta wa wasu ‘yan kasuwa rage farashinsu da kusan N100, duk da hakan na iya jawo musu asara sosai..

Dangote ya rage farashin man fetur

Aliko Dangote ya bayyana a wani taron manema labarai cewa yana da bayanai kan yunkurin wasu ‘yan kasuwa na ci gaba da sayar da fetur da tsada duk da rage farashin da ya yi.

Vanguard ta wallafa cewa saboda haka ya jaddada cewa za a tilasta sabon tsarin farashi, inda MRS zai fara sayarwa a kan N739 a Najeriya.

Dangote ya ce an bude kofa ga mambobin IPMAN da sauran masu karfin saye su zo su dauki man fetur a kan N699, yana mai bayyana aniyarsa ta sauke farashin domin kada a sayar da fetur sama da N740 a watan Disamba da Janairu.

'Yan kasuwa sun sauke farashin litar fetur

Bincike ya nuna cewa rage farashin MRS ya jawo dogayen layukan motoci a wasu wurare a Lagos, musamman Alapere, inda masu mota suka fi zabar gidajen da ke sayarwa da araha fiye da wadanda ke sama da N800.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An fara neman a tsige Bola Tinubu daga kujerar shugaban kasa

Sakamakon haka, wasu gidajen mai sun fara rage farashi domin samun kwastomomi. A Ogun, wasu sun sauke farashi zuwa N750 ko kasa da N800, yayin da wasu har yanzu ke fama da karancin masu saye saboda tsadar farashi.

Masu shigo da mai na tafka asara

Rahotanni sun nuna cewa rage farashin na jawo asara mai tsanani ga ‘yan kasuwa da masu shigo da mai daga kasashen waje.

NNPCL ma ya rage farashi daga N875 zuwa tsakanin N825 da N840, duk da cewa kudin da yake kashewa wajen shigo da mai ya kai kusan N828 kan kowace lita.

Matatar Dangote da ke jihar Legas
Matatar Dangote da ke jihar Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Mai magana da yawun IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce ‘yan kasuwa za su iya rasa fiye da N80bn, yana mai kira ga matatar Dangote da ta duba hanyoyin rage radadin asara, ciki har da rangwamen saye a nan gaba.

Farashin mai ya sauka a Gombe

Wani ma'aikacin gwamnati a jihar Gombe, Malam Adam Abdallah Hamza ya ce ya ga alamun fara rage kudin lita a gidajen mai.

Malam Hamza ya ce:

"Lallai da na je gidan mai na samu sauki. Duk da cewa farashin ya bambanta tsakanin gidajen mai.

Kara karanta wannan

Yadda Donald Trump ya jawo wa Najeriya asarar kusan Naira tiriliyan 1

'Ana samun sauki ba kamar kwanakin baya ba."

Wani dalibin jami'a, Nura Ahmad ma ya bayyana wa Legit cewa yana farin ciki da gogayyar da ake tsakanin Dangote da 'yan kasuwa.

Ya ce:

'Ina farin ciki da hakan matukar za a cigaba da samun sauki. Ina fatan za a cigaba da rage kudin mai."

IPMAN ta ce farashin man fetur zai ragu

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa, IPMAN ta ce ta kulla yarjejeniya da matatar Dangote da ke Legas.

Shugabannin kungiyar sun ce yarjejeniyar za ta jawo raguwar farashin mai a Najeriya kuma jama'a za su samu saukin rayuwa.

A karkashin bayanin da suka yi, jagororin IPMAN sun bukaci mambobin kungiyar da su fifita sayen mai a matatar Dangote.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng