An Yi Asara: Gobara Ta Lakume Wata Babbar Kasuwa a Kano

An Yi Asara: Gobara Ta Lakume Wata Babbar Kasuwa a Kano

  • An samu asarar dukiya mai tarin yawa bayan barkewar gobara a wata kasuwar kayan gado da ke jihar Kano
  • Gobarar ta tashi ne a kasuwar kayan gado ta Sabuwar Lale da ke cikin karamar hukumar Gwale, inda ta kone dukiya ta miliyoyin Naira
  • 'Yan kasuwar da lamarin ya shafa sun yi kira ga gwamnati kan ta kawo musu dauki sakamakon girman asarar da suka yi

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - An shiga jimami bayan gobarar da ta barke a wata kasuwa da ke jihar Kano ta jawo babbar asara.

Gobarar ta auku ne a kasuwar kayan gado ta Sabuwar Lale da ke Tal’udu, a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Gobara ta lakume shaguna a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta kawo tsarin da zai kara sauke farashin fetur a gidajen mai a Najeriya

Gobara ta yi barna a Kano

Gobarar ta bazu cikin sauri a faɗin kasuwar, ta cinye shaguna da dama kafin isowar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano.

Wani ɗan kasuwa da lamarin ya shafa, Bashir Ustaz, ya ce ya shiga ruɗani matuƙa lokacin da ya isa kasuwar ya tarar da shagonsa ya kone kurmus.

"Da misalin karfe 3:00 na dare aka kira ni aka shaida min cewa gobara ta tashi a kasuwa. Da na iso, abin da na gani ya sa na rufe idona. Wuta ta lalata dukiyata gaba ɗaya."

- Bashir Ustaz

Ya kara da cewa kwana guda kafin faruwar lamarin, kasuwar cike take da cunkoso da harkokin kasuwanci, amma zuwa safiya komai ya koma toka.

An yi asarar miliyoyi

Mataimakin shugaban kasuwar, Adamu Mansur, wanda aka fi sani da Madaki, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare kuma ta ci gaba har zuwa wayewar gari.

"Wutar ta fara da misalin karfe 2:30 na dare har zuwa safiya. Muna rokon Allah Ya maye mana gurbin asarar da wani abu mafi alheri.”

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke bokaye da kudin kasashen waje na boge bayan damfarar 'yan Najeriya

- Adamu Mansur

Madaki ya bayyana cewa har yanzu ’yan kasuwar ba su iya kididdige adadin asarar da suka yi gaba ɗaya ba, amma ya ce wasu shaguna sun yi asarar kayan ɗaki da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.

"A shagona kaɗai, ina da sama da kayan ɗaki guda 40 da aka shirya kai wa yau. Guda huɗu daga ciki darajarsu ta haura Naira miliyan 5, yayin da wasu guda uku darajarsu ta wuce Naira miliyan 4.”

- Adamu Mansur

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da kuma masu hannu da shuni da su tallafa wa ’yan kasuwar da lamarin ya shafa, la’akari da girman asarar da aka yi.

Gobara ta kona shaguna a kasuwar Kano
Motocin kashe gobara na hukumar 'yan kwana-kwana Hoto: @fedfireng
Source: Twitter

Gobara ta kona shaguna masu yawa

Rahotanni sun nuna cewa akalla shaguna na dindindin 11 da kuma kusan gine-ginen wucin gadi 20 ne suka kone gaba ɗaya.

Jami’an kashe gobara sun yi ta kokarin kashe wutar na tsawon awanni da dama kafin su samu nasarar shawo kanta bayan sallar Asuba.

Kara karanta wannan

Bayan zama da DSS, Abba ya yi nasarar hana Ganduje kafa Hisbah a Kano

Ko da yake babu wanda ya rasa ransa, ’yan kasuwar sun ce gobarar ta katse musu babbar hanyar samun abin rayuwa.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma ba kan musabbabin gobarar.

Gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura da ke birnin tarayya Abuja.

Gobarar ta fara ne daga farantin solar da aka sanya a saman ɗaya daga cikin gine-ginen kafin ta bazu cikin gaggawa zuwa sauran gidajen da ke kusa.

Mummunar gobarar ta lalata dukkan kayayyakin cikin gidajen da abin ya shafa, ciki har da kayan daki, tufafi, kayan abinci da sauran muhimman abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng