‘Shirya Komai Aka Yi’: An ‘Gano’ yadda Rashin Tsaro Ya Fara a Najeriya
- Tsohon sakataren Afenifere, Pa Ayo Opadokun, ya ce matsalar tsaro a Najeriya shiri aka yi mata tun tuni, ba kuskure ba ne
- Opadokun ya bayyana cewa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda na samun tallafi daga wasu ‘yan Najeriya da kuma masu son tayar da zaune tsaye
- Tsohon jagoran NADECO ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan tsauraran matakan tattalin arziki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Tsohon sakataren kungiyar Afenifere ta Yarbawa kuma jigo a NADECO, Pa Ayo Opadokun, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.
Dattijon ya ce rashin tsaro na addabar wasu sassan Najeriya wanda aka shirya tun da dadewa, ba wai ya zo ne bisa kuskure ba.

Source: Facebook
Dattijo ya yi zarge-zarge kan ta'addanci
Opadokun ya bayyana hakan ne yayin da ake nadin sa a matsayin babban mai ba da shawara (Grand Patron) na kungiyar CAN reshen karamar hukumar Offa a jihar Kwara, cewar Tribune.
Ya ce ‘yan bindiga da ‘yan tada kayar baya na samun tallafi daga mutane daban-daban lamarin da ya ki ci yaki cinyewa.
A cewarsa:
“Wasu ‘yan Najeriya, ciki har da wakilan da ke son tarwatsa kasa da kuma wadanda ba sa son wannan gwamnati, sun dauki manyan matakai tun da dadewa domin jefa Najeriya cikin rikici.”
Tsohon dattijon ya bayyana halin tsaro a kasar a matsayin abin damuwa sosai, yana mai cewa an taba gargadin gwamnati kan hatsarin barin ‘yan sa-kai su rika amfani da makamai da suka fi na sojojin kasa karfi.
Ya ce ba tare da tsoro ba zai iya cewa a watan Agustan 2022, a wani taro da ya dauki kwanaki hudu a Nicon Hilton, wasu ‘yan Najeriya tare da kungiyoyi daga yankin Sahel sun tsara yadda za su mamaye Najeriya.
“Yanzu muna ganin sakamakon. Abin da El-Rufai ya fada duk mun ji. Wannan halin da ake ciki ba haka kawai ba ne, shiri ne.”
- Pa Ayo Opadokun

Source: Facebook
Shawarar da aka ba gwamnatin tarayya kan tsaro
Opadokun ya shawarci gwamnatin tarayya da kada ta sassauta yaki da ‘yan ta’adda, yana mai cewa bai kamata a nuna tausayi ga ‘yan bindiga da masu daukar nauyinsu ba.
Ya kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa kan manufofin tattalin arziki, yana cewa shugaban kasa na kokarin aiwatar da cikakken tsarin tarayya ta fuskar kudade.
Ya ce dokar gyaran haraji za ta yi tasiri sosai, inda ya bayyana cewa daga watan Janairu mai zuwa, mutane da dama ba za su biya haraji ba saboda karancin abin da suke samu, cewar Vanguard.
Tinubu ya kawo sabon tsarin tsaro
Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabon tsari na yaƙi da ta’addanci a Najeriya baki daya.
Tinubu zai ayyana ’yan bindiga, masu garkuwa, masu karɓar kuɗin fansa da masu taimaka musu a matsayin ’yan ta’adda.
Shugaban ya ce manufar ita ce kare zaman lafiyar ƙasa, rage fargabar jama’a da tabbatar da sakamako mai gamsarwa daga kuɗaɗen tsaro.
Asali: Legit.ng

