Musa Kamarawa Ya Yi Rantsuwa da Alkur’ani kan Zargin Matawalle game da Ta’addanci

Musa Kamarawa Ya Yi Rantsuwa da Alkur’ani kan Zargin Matawalle game da Ta’addanci

  • Tsohon hadimin Bello Matawalle ya sake bayyana kansa kan zargin alakar ministan da ta’addanci a bidiyon da ya tayar da kura
  • A bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, Kamarawa ya ce bai aikata wani abu da kansa ba a zamanin mulkin Matawalle
  • Musa Kamarawa ya rantse da Alƙur’ani Mai Girma, yana kalubalantar Matawalle da masu musun zargin da su rantse idan suna zarginsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Tsohon hadimin Bello Matawalle ya sake yin magana game da zargin ministan da alaka da ta'addanci wanda ake ta magana a kai.

Musa Kamarawa a kwanakin baya ya tayar da kura bayan fitar da wani bidiyo da ya ke alakanta Matawalle da yan ta'adda lamarin da ya tayar da kura.

Musa Kamarawa ya sake yin bidiyo game da zargin Matawalle
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani bidiyo da shafin Abdullahin Gwansu TV ya wallafa a Facebook a yau Lahadi 21 ga watan Disambar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, jigonta kuma tsohon kwamishina yar bar duniya

Matawalle: Kamarawa ya sake tone-tone a bidiyo

A cikin faifan bidiyon, Kamarawa ya tabbatar da cewa bai taba yin wani abu a lokacin mulkin Matawalle a karan kansa ba.

Tsohon hadimin Matawalle ya yi rantsuwa da Alkur'ani mai girma kan abubuwan da suka faru a wancan lokaci na mu'amala da yan bindiga.

Ya ce:

"Ni Musulmi ne, kuma wannan Alkur'ani ne mai tsarki, kuma bai barin bashi, Allah shi yasan yadda yake bi ya saka wa mutum.
"Allah na roke ka, idan duk abin da na yi, ba Matawalle ba ne ya saka, ka da Allah ya sa na gama rayuwa ta lafiya.
"Idan Dr Matawalle yana inkari, ko kuma wasu suna inkari kan cewa abin da na fada ba gaskiya ba ne, su zo su yi rantsuwa da Alkr'ani cewa ni na saka kaina."
An kuma kalubalantar Matawalle kan alaka da yan ta'adda
Tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Original

Kalabalen da Kamarawa ya tura ga Matawalle

Musa Kamarawa ya kara cewa bai taba yin wani abu ba, ba tare da saka hannun tsohon gwamnan Zamfara ba a wancan lokacin da yake hadiminsa.

Kara karanta wannan

An lakaɗawa Kansila duka kan zargin ba shi kuɗi ya mari na kusa da Gwamna

Ya kuma kalubalanci Matawalle da sauran masu zargin karya yake yi da su fito su rantse kamar yadda ya yi a yanzu.

"Saboda haka babu wani abu billahil lazi babu wani abu da na aikata ba tare da hannun Bello Matawallen Maradun ba.
"Idan ba haka ba, ya fito da mukamin da ya ba ni na hadiminsa ya ce karya nake yi, na aikata kaza na aikata kaza."

- Musa Kamarawa

Bello Turji ya magantu kan alaka da Matawalle

Mun ba ku labarin cewa shedanin dan bindiga, Bello Turji ya fito da sabon bidiyo yana karyata zargin cewa Bello Matawalle ya ba ’yan bindiga kudi.

Turji ya mayar da martani ne ga tsohon hadimin Matawalle, Musa Kamarawa, yana zarginsa da ƙarya game da cewa tsohon gwamnan ya ba su kudi.

Duk da bayyana kiyayya ga Matawalle, Turji ya ce ba zai yarda a yi amfani da sunansa wajen bata suna wani ba saboda hakan bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.