Jerin Mutane, Kungiyoyi 31 da Tinubu Zai Ayyana Yan Ta’adda a Sabon Tsarin Tsaro
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabon tsari na yaƙi da ta’addanci a Najeriya baki daya
- Tinubu zai ayyana ’yan bindiga, masu garkuwa, masu karɓar kuɗin fansa da masu taimaka musu a matsayin ’yan ta’adda
- Shugaban ya ce manufar ita ce kare zaman lafiyar ƙasa, rage fargabar jama’a da tabbatar da sakamako mai gamsarwa daga kuɗaɗen tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsaron Najeriya ya shiga sabon salo bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabuwar manufar yaƙi da ta’addanci.
Sabon tsarin ya sake fayyace waɗanda za a ɗauka a matsayin ’yan ta’adda a ƙarƙashin dokar ƙasa.

Source: Twitter
Sabon tsarin tsaron Tinubu a Najeriya
A sabon umarnin, gwamnatin tarayya ta ayyana ƙungiyoyin ɗauke da makamai, masu garkuwa da mutane, masu karɓar kuɗin gayya, da duk masu ba su taimako a matsayin ’yan ta’adda, cewar Punch.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabin kasafin kuɗin ƙasa, inda ya ce gwamnati na zuba jari a harkar tsaro.
Ya jaddada cewa sabon tsarin zai sauya gaba ɗaya yadda Najeriya ke fuskantar ta’addanci da laifuka masu amfani da makamai.
Ya ce masu garkuwa da fararen hula da ƙungiyoyin da ke tilasta wa al’umma biyan kuɗi za a yi musu hukunci a matsayin ’yan ta’adda.
Haka kuma, duk wanda ya mamaye ko ya yi yunƙurin mamaye wani yanki na ƙasar Najeriya ta hanyar amfani da ƙarfi, zai fuskanci wannan hukunci.

Source: Facebook
Mutane, kungiyoyi da za a ayyana yan ta'adda
Wani masanin harkokin tsaro a Najeria ya wallafa jerin wadanda za su iya shiga cikin yan ta'addan a kasar.
Matashin ya wallafa haka a shafinsa na X inda ya ce a sabon tsarin, za a saka su cikin yan ta'adda a Najeriya.
A sabon tsarin, mutanen sun haɗa da:
- Ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai ba tare da ikon gwamnati ba
- Mutanen da ke amfani da makamai masu hatsari ba tare da izini ba
- ’Yan bindiga
- Mayaƙan sa-kai (militias)
- Ƙungiyoyin ’yan daba masu makamai
- Ƙungiyoyi masu amfani da makamai
- ’Yan fashi da makami
- Ƙungiyoyin asiri
- Ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke zaune a dazuka
- Sojojin haya masu alaƙa da ƙasashen waje
- Masu tayar da hankali a siyasa
- Masu tayar da rikicin ƙabilanci
- Masu aikata tashin hankali don kuɗi
- Masu tayar da rikicin addini
- Masu garkuwa da mutane
- Masu tilasta karɓar kuɗi
- Masu ɗaukar nauyin ƙungiyoyin makamai
- Masu sarrafa kuɗaɗen ƙungiyoyin ta’addanci
- Masu ɓoye ’yan ta’adda
- Masu ba da bayanan sirri (’yan leƙen asiri)
- Masu taimakawa biyan kuɗin fansa
- Masu shiga tsakani wajen tattaunawar kuɗin fansa
- ’Yan siyasar da ke kare ’yan ta’adda
- ’Yan siyasar da ke shiga tsakani don kare ayyukan tashin hankali
- Masu jigilar mayaƙa ko makamai
- Masu sayar da makamai
- Masu ba da mafaka
- ’Yan siyasar da ke ƙarfafa tashin hankali
- Sarakunan gargajiya da ke tallafa wa ta’addanci
- Shugabannin al’umma da ke taimaka wa tashin hankali
- Shugabannin addini da ke kare ko halasta ta’addanci.

Kara karanta wannan
Bayan takunkumin Amurka, Trump ya kara saka doka ga 'yan Najeriya da wasu kasashe
Tinubu ya sha alwashin kakkabe yan ta'adda
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin ci gaba da yaki da ta'addanci domin tabbatar da samun zaman lafiya.
Tinubu ya nuna cewa babu sassauci ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin kasar.
Shugaban ya ce gwamnati za ta tabbatar da daidaiton tattalin arziki da tsaro mai ɗorewa a Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng
