Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi Sun Sanar da Tinubu Boyayyen Lamari kan Marigayin

Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi Sun Sanar da Tinubu Boyayyen Lamari kan Marigayin

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta'aziyya kan rasuwar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • A yayin ziyarar, iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun godewa shugaban kasar kan samun lokaci domin zuwa yi musu ta'aziyya
  • Hakazalika sun bayyanawa Shugaba Bola Tinubu wasu abubuwa kan rayuwar marigayin wanda ya riga mu gidan gaskiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Iyalan fitaccen malamin addinin Musulunci, marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, sun bayyana mutanen da suka amfani da koyarwarsa.

Iyalan sun bayyana cewa mahaifinsu ya yi jagoranci tare da tarbiyya ga Musulmi sama da miliyan 63 a fadin Najeriya da wasu sassan duniya a tsawon rayuwarsa.

Tinubu ya je ta'aziyyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce magajin marigayin, Khalifa Sheikh Ibrahim Shaykh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana hakan ranar Asabar, 20 ga watan Disamban 2025 a Bauchi.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fada a gidan Dahiru Bauchi bayan saka wa jami'a sunansa

Ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya biyo bayan rasuwar babban malamin addinin.

An sanar da Tinubu abubuwa kan Dahiru Bauchi

A cewar Khalifa Ibrahim, tsawon shekaru sama da 56, marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance yana shirya taron addinin Musulunci tsakanin biyar zuwa 10 duk shekara.

Ya ce kowanne taro na janyo miliyoyin mabiya, almajirai, dalibai, masoya da masu kauna, wanda adadinsu ya haura miliyan 63.

Hakazalika ya jaddada cewa duk da wannan dumbin mabiya da yake da su, babu wani tarihi a Najeriya daga 1969 zuwa 2025 da ke nuna cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya taɓa haddasa tashin hankali, rikici ko tayar da tarzoma.

Iyalan Dahiru Bauchi sun yabawa Tinubu

A cikin wani sako daga iyalan, wanda Dr. Bashir Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya karanta, ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu bisa yadda ya kai ziyara da kansa.

An kuma yabawa Tinubu kan yadda ya tura manyan jami’an gwamnati domin wakiltarsa a jana’iza da binne gawar marigayin a ranar 28 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rada wa babbar jami'a a Najeriya sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

"Dukkan iyalai 820 na Sheikh Dahiru Usman Bauchi, OFR, tare da ’ya’yansa 82 da ke raye, da kuma mabiya, almajirai, dalibai, masoya da mabiyansa sama da miliyan 63, suna maraba da kai tare da gode maka bisa jajircewa, biyayya da tausayinka a wannan lokaci na alhini.”

- Dr. Bashir Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Iyalan Dahiru Bauchi sun yabawa Shugaba Bola Tinubu
Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Dahiru Bauchi ya bar iyalai da dama

Da suke waiwaye kan rayuwarsa, iyalan sun bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutum da ya rayu tsawon shekaru 101, watanni biyar da kwana uku, inda ya sadaukar da rayuwarsa wajen addini, ilimi, zaman lafiya da haɗin kai.

Sun kuma bayyana cewa marigayin ya haifi ’ya’ya 100, maza 50 da mata 50 daga cikinsu 82 na raye. Sun kara da cewa ’ya’yansa 84 (maza 42 da mata 42) sun haddace Alƙur’ani Mai Girma.

Iyalan sun kuma bayyana cewa zuriyar Sheikh Dahiru Bauchi ta haɗa da jikoki 512 da 'ya'yan jikoki 206, wanda hakan ya kai jimillar iyalansa zuwa mambobi 820.

Tinubu ya karrama Sheikh Dahiru Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Shugaba Bola Tinubu ya karrama marigayin ta hanyar canza sunan jami’ar kimiyyar lafiya ta tarayya da ke Azare, jihar Bauchi.

Mai girma shugaban kasar ya canza sunan jami'ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Health Sciences, Azare, a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng