NMDPRA: Hukumar ICPC Ta Gayyaci Attajiri, Aliko Dangote kan Zarge Zarge
- Zargin da attajiri, Alhaji Aliko Dangote kan tsohon shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed ya fara daukar wani sabon salo
- Hukumar ICPC ta gayyaci Aliko Dangote domin bayar da ƙarin bayani game da ƙarar da ya shigar kan tsohon shugaban NMDPRA
- Dangote ya zargi Farouk da cin hanci, almundahana da kashe sama da dala miliyan bakwai wajen karatun ’ya’yansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaƙa da Hakan, wato ICPC, ta gayyaci Alhaji Aliko Dangote zuwa ofishinta.
Hukumar ta yi gayyatar domin ya ba da ƙarin bayani dangane da ƙarar da ya shigar kan tsohon shugaban hukumar NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed.

Source: Twitter
Dalilin gayyatar Dangote da ICPC ta yi
Ana sa ran Dangote zai bayyana gaban ICPC ko kuma ya aike da lauyansa, Ogwu Onoja (SAN), a gobe Litinin 22 ga watan Disambar 2025, ranar da hukumar za ta fara binciken ƙarar, cewar The Nation.
Majiyoyi sun ruwaito cewa ICPC ta kafa kwamitin ƙwararrun masu bincike tun ranar Juma’a 19 ga watan Disambar 2025 domin gudanar da binciken.
Majiyoyi sun bayyana cewa hukumar ta bukaci Dangote ya miƙa dukkan hujjoji da takardun shaidar da ke goyon bayan ƙarar ga hukumar yaki da cin hanci.
A ƙarar da ya shigar, Dangote ya zargi Farouk da cin hanci da almundahanar kuɗaɗen gwamnati, ciki har da kashe miliyoyin daloli wajen karatun ’ya’yansa huɗu a manyan makarantu masu tsada a ƙasar Switzerland.
Dangote ya kuma zargi Farouk da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, ta hanyar raunana matatun mai na cikin gida.
Farouk Ahmed ya riga ya yi murabus daga muƙaminsa, amma ICPC ta ce murabus ɗin ba zai hana ci gaba da binciken ba.
“Dukkan shirye-shirye sun kammala domin fara bincike,”
- In ji wata majiya daga ICPC

Source: Getty Images
NMDPRA: Umarnin da shugaban ICPC ya bayar
Majiyar ta ce Shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu (SAN), ya umarci tawagar binciken da su ajiye sauran ayyuka su mayar da hankali kacokan kan ƙarar Dangote.
Ta ce Dangote ko lauyansa za su zo su amince da ƙarar a hukumance, tare da gabatar da duk wasu muhimman takardu da hujjoji.
ICPC ta ce ta riga ta amince da karɓar ƙarar cikin sa’o’i 48, kamar yadda doka ta tanada, cewar rahoton TheCable.
Bayan amincewa da ƙarar, ICPC za ta ware muhimman batutuwa sannan ta bukaci Farouk Ahmed ya ba da amsa kan zarge-zargen da ake masa.
Majiyar ta ce duk da tambayoyi da ake yi daga jama’a, hukumar za ta yi adalci ga dukkan ɓangarori.
Ta kara da cewa murabus ɗin Farouk ba zai shafi binciken ba, domin batun yana cikin abin da ya shafi moriyar al’umma.
Oshiomhole ya bukaci rataye Farouk Ahmed
Kun ji cewa Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya yi murnar murabus din shugabannin NMDPRA da NUPRC daga mukamansu.
Oshiomhole ya ce ya ji dadi ne saboda haka ya zama dole domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga rugujewa.
Sanata David Jimkuta ya goyi bayan sanatan yayin tantance sababbin shugabannin hukumomin da Bola Tinubu ya tura.
Asali: Legit.ng

