Musulunci Ya Yi Rashi: Shugaban Masallacin Annur Ya Rasu, Pantami Ya Yi Ta'aziyya
- Allah ya yi wa shugaban Masallacin Annur da ke babban birnin tarayya Abuja, Dr. Kabiru Usman Kabo rasuwa
- Marigayi Dr. Kabiru Usman Kabo ya rasu ne a gidansa da ke birnin Manchester bayan ya yi fama da jinya a kasar Ingila
- Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Ali Isah Ibrahim Pantami ya yi ta'aziyyar marigayin wanda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - An yi babban rashi bayan rasuwar shugaban masallacin Annur da ke birnin tarayya Abuja, Dr. Kabiru Usman Kabo.
Marigayin ya yi bankwana da duniya ne a gidansa da ke birnin Manchester na kasar Birtaniya.

Source: Facebook
Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da rasuwar marigayin a shafinsa na Facebook.
Farfesa Isa Ali Pantami wanda ke gabatar da karatu da Tafsiri a Masallacin Annur ya sanar da cewa Allah Ya yi masa cikawa ne a ranar Asabar, 20 ga watan Disamba, 2025.
Tsohon Ministan ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a gidansa da ke birnin Manchetster na kasar Birtaniya, bayan fama da jinya.
Farfesa Pantami ya yi ta'aziyya
"Ina mika ta’aziyyata ga iyali, abokai, ’yan uwa, abokan aiki da kuma daliban Malam Kabiru Usman Kabo, PhD, wanda ya rasu a gidansa da ke Manchester, a kasarsa ta biyu, Ingila, a yammacin ranar Asabar, 20 ga Disamba, 2025. Allah Ya sanya Aljannah ta zama makoma a gare shi."
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami
Farfesa Pantami ya ce ziyarce shi tare da iyalinsa a gidansu da ke Manchester, inda ya je da matarsa tare da dalibinsa, Dr. Salim Abatcha, Amir na Nigeria Muslim Forum (NMFUK), reshen Manchester, da Injiniya Ibrahim Yakub Nguru.
Tsohon Ministan ya ce iyalan marigayin sun karɓe su da matuƙar karamci da girmamawa.
"Mun tattauna da shi sosai. Ya sanar da mu cewa likitocinsa sun yi hasashen rasuwarsa tun fiye da watanni 10 da suka gabata. Alhamdu lillahi! Duk da rashin lafiyarsa, ya ce yana jin sauƙi sosai, kuma yana jin karfin jikinsa."
"Haka kuma, na karfafa masa gwiwa da ya ci gaba da jajircewa. Masana na iya yin hasashe a fannoninsu, amma Allah Maɗaukakin Sarki Shi kaɗai Ya san lokacin rasuwar kowane rai da cikakken tabbaci. Ya tabbatar da hakan da abin da ya gani a rayuwarsa."
Dr. Kabiru Kabo ya kasance jagora kuma malami ga mutane da dama tsawon fiye da shekaru 35. Ya koyar a cibiyoyi daban-daban, ciki har da Jami’ar Manchester.
Ya kasance shugaban ICICE Wuse 2 Abuja ciki har da Masallacin Annur da ke Wuse 2 Abuja har zuwa rasuwarsa.
Yaushe za a yi jana'izar Dr. Kabiru Usman Kabo?
Farfesa Pantami ya bayyana cewa za a yi jana'izar marigayin a ranar Lahadi, 21 ga watan Disamban 2025 a birnin Manchester na kasar Ingila.

Source: Facebook
Tsohon Ministan ya ce marigayin ya sha wahala matuka a lokacin rashin lafiyarsa, amma ya kasance mai hakuri da juriya, yana mai dogara ga Allah.
"Allah Ya sanya Dr. Kabiru Kabo cikin waɗanda mutuwarsu hutu ce daga wahalhalun duniya, kuma ya koma ga rahamar Allah. Allah Ya karɓe shi a Aljannatul Firdausi. Allah Ya ba iyalinsa da mu baki ɗaya juriyar jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba."
"Sai mun haɗu, ya ɗan’uwa, a wuri inda ba za mu ƙara rabuwa ba."
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami
Shugaban Izalah ya rasu a Gombe
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Izalah reshen jihar Gombe ta sanar da rasuwar daya daga cikin shugabanninta.
Kungiyar Izalah a madadin shugabanta, ta bayyana alhini kan rashin jajirtaccen malamin Alhaji Abdullahi Barde wanda ya ba da gudunmawa.
Hakazalika, kungiyar ta yi addu'a ga marigayin da fatan Allah ya jikansa ya gafarta masa ya kuma ba iyalansa hakurin rashi.
Asali: Legit.ng


