Gwamantin Kebbi na da Hannu a Matsalar Malami da EFCC? Gwamna Ya Yi Martani
- Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi karin haske kan zargin tana hannu game da matsalolin Abubakar Malami a hukumar EFCC
- Gwamna Nasir Idris ya musanta zargin cewa akwai hannun gwamnatin a binciken EFCC da ake yi wa tsohon ministan
- An bayyana cewa tsare Malami ya zo ne bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kebbi a 2027
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi magana bayan zarge-zargn cewa tana da hannu game da binciken da ake yi kan Abubakar Malami.
Gwamnatin ta musanta zargin da ke yawo cewa ita ce ke da hannu a matsalar da tsohon Ministan Shari’a, Malami ke fuskanta a hannun EFCC.

Source: Facebook
Gwamnatin ta bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen da ake bincike a kansu game da Malami ba daga gwamnatin jihar suka fito ba, cewar Punch.
Tuhumar da EFCC ke yi wa Malami
An gayyaci Malami zuwa ofishin EFCC ne a ranar 28 ga Nuwamba, dangane da batutuwan da suka shafi kwato dukiyar Abacha a lokacin da yake rike da mukamin Lauyan Ƙasa.
A ranar 29 ga Nuwamba, Malami ya bayyana cewa tambayoyin da EFCC ta yi masa sun kasance masu amfani, inda ya ce zarge-zargen da ake masa ƙirƙira ne.
Sai dai, ya koma EFCC a ranar 8 ga Disamba, kuma tun daga lokacin yake tsare a hannun hukumar, bayan da aka ruwaito cewa bai cika sharuddan beli ba.
An kama Malami ne kwanaki kaɗan bayan da ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaɓen 2027.
Rahotanni sun bazu a shafukan sada zumunta suna cewa batun EFCC na iya kasancewa na siyasa, musamman ganin rikicin da ya taso tsakanin Malami da gwamnatin Kebbi kan matsalar tsaro.
Martanin gwamnatin Kebbi kan zargin Malami
Sai dai, Ahmed Idris, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Nasir Idris, ya karyata wannan zargi, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.
Kakakin gwamnan ya ce:
“Babu gaskiya a hakan. Gwamnatin Jihar Kebbi ba ta da hannu a matsalar Malami; batun ya faro tun kafin wannan gwamnati ta hau mulki.
“An shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama a kansa ne bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna. Kuma ƙorafe-ƙorafen ba daga Kebbi suka fito ba, daga Abuja suka fito, daga wasu abokan aikinsa.
“Duk wanda ya ce gwamnatin Kebbi na da hannu a batun Malami, makaryaci ne kuma mai mugun nufi, domin gwamnatin jihar ma ba ta san ainihin abin da ke faruwa da shari’arsa ba.”
EFCC ta kai samame gidan 'yar Buhari
A wani labarin, hukumar EFCC ta kai samame zuwa wani gida da ke da alaƙa da tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami.
An ce ’yar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tana cikin gidan a lokacin da jami’an suka kai samamen, wannan zai ƙara jan hankalin jama’a.
Matakin ya zo ne yayin da bincike ke ci gaba kan zarge-zargen da suka shafi kuɗi da ayyukan ofishin Malami a lokacin da ya ke ministan shari'a.
Asali: Legit.ng

