An Sanya Dokoki a Gari saboda Ziyarar da Bola Tinubu Zai Kai Gidan Sheikh Dahiru Bauchi
- Gwamnatin Bala Mohammed ta rufe wasu hanyoyi tare da sauya akalar wasu a birnin Bauchi gabanin isowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Ana sa ran Shugaba Tinubu zai kai ziyara gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin yi wa iyalansa ta'aziyya a yau Asabar
- Mai magana da yawun gwamnan Bauchi ya bukaci jama'a su bai wa jami'an tsaro hadin kai domin tabbatar da komai ya tafi cikin kwanciyar hankali
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da rufe wasu manyan hanyoyi tare da karkatar da zirga-zirgar ababen hawa zuwa wasu tituna daban a cikin birnin Bauchi.
Gwamnatin ta dauki wannan matakai ne domin tabbatar da tsaro gabanin ziyarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kai jihar Bauchi yau Asabar.

Source: Twitter
Bola Tinubu zai kai ziyara gidan Dahiru Bauchi
A wata sanarwa da ta wallafa a X, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Shugaba Tinubu zai kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Sheiikh Dahiru Usman Bauchi a yau Asabar.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai jajanta wa iyalai da mabiya marigayi fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Bisa haka ne gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta sanar da rufe wasu manyan hanyoyi, tare da canza wa matafiya hanya a cikin kwaryar birni.
Ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Mukhtar Gidado, mai bai wa Gwamna Bala Mohammed shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar a daren Juma’a.
Matakan da gwamnatin Bauchi ta dauka
Sanarwar ta ce za a rufe manyan hanyoyin da ke kai wa masallacin marigayi Dahiru Bauchi da wasu muhimman wurare ko kuma larkatar da masu bin titunan daga ƙarfe 1:00 na rana zuwa 6:00 na yamma.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya rada wa babbar jami'a a Najeriya sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Gidado ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin dalilai na tsaro da sauƙaƙa zirga-zirga yayin ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hadimin Gwamna Bala ya bayyana cewa matakin ya zama dole ne domin kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da ziyarar Shugaban Ƙasa ta gudana cikin kwanciyar hankali.

Source: Twitter
Ya bukaci al’ummar jihar Bauchi da su shirya tafiye-tafiyensu tun da wuri, su bi umarnin jami’an tsaro da na zirga-zirga, tare da kauce wa wuraren da aka kayyade, in ji rahoton Leadership.
Gwamnatin jihar ta kuma roƙi jama’a da su kasance masu natsuwa da bada haɗin kai ga jami’an tsaro, tare da neman afuwar duk wata matsala da matakin ka iya haifarwa.
“Gwamnatin Jihar Bauchi na gode wa al’umma bisa fahimta da haɗin kai,” in ji sanarwar.
Tawagar Kaduna ta je gidan Dahiru Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya jagoranci tawagar gwamnatin Kaduna zuwa gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin yin ta'aziyya.
Malam Uba Sani ya yi alkawarin kafa wata gidauniya domin tunawa da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ci gaba da ayyukan alherin da ya saba yi.
Ya ce gwamnatin Kaduna za ta kafa wani kwamiti da zai kunshi ‘ya'yan marigayi Sheikh, dalibansa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tsara cikakkun bayanan kafa gidauniyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
