Gwamna Uba Sani Ya Yi Wa Malaman Makaranta Gata a Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya waiwayi malaman makaranta da ke aikin koyar da dalibai a makarantun gwamnati
- Sanata Uba Sani ya amince da tsawaita lokacin da malamai za su yi ritaya daga shekara 60 zuwa 65 a fadin jihar
- Hakazalika, gwamnan ya fito da tsarin ba da alawus ga malaman da aka tura yankunan karkara da wurare masu wahalar zuwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan ihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya amince da inganta sharuddan aiki ga malamai a faɗin jihar.
Gwamna Uba Sani ya amince da tsawaita lokacin yin ritayar malaman makaranta a fadin jihar Kaduna.

Source: Facebook
Uba Sani ya tsawaita lokacin ritayar malamai
Tashar Channels tv ta ce kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya bayyana hakan.
Daga ranar 1 ga Agusta, 2025, an tsawaita shekarun ritayar dole ga malamai daga shekara 60 zuwa 65, yayin da iyakar shekarun aiki kuma aka kara su daga shekara 35 zuwa 40.

Kara karanta wannan
Gwamna Fubara ya fadi biliyoyin da ya tarar a asusun Rivers bayan cire dokar ta baci
A cewar kwamishinan, malamai da aka tura zuwa yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa za su rika karɓar alawus na musamman.
Ahmed Maiyaki ya bayyana cewa wannan amincewa ta yi daidai da dokar daidaita shekarun ritayar malamai ta 2022, wadda majalisar tarayya ta amince da ita, jaridar TheCable ta kawo labarin.
Dokar ta ware malamai daga tsarin ritayar ma’aikatan gwamnati na shekara 60 ko shekaru 35 na aiki, domin girmama muhimmiyar rawar da suke takawa wajen bunkasa ci gaban kasa.
Ya kara da cewa an fitar da wata takardar umarni daga ofishin gwamna, wadda babbar sakatariya, Felicia I. Makama, ta sanya wa hannu, inda aka umurci dukkan hukumomin da abin ya shafa su bi wannan umarni.
Meyasa Uba Sani ya dauki matakin?
A cewarsa, wannan mataki yana nuna kwarin gwiwar Gwamna Sani wajen inganta jin daɗin ma’aikata da kuma farfaɗo da fannin ilimi a jihar.
Ya lura da cewa gwamnan na kallon ƙwararrun malamai a matsayin ginshikai wajen samar da ingantaccen ilimi da kuma dorewar fannin koyarwa a duk faɗin jihar.
Takardar umarnin ta kuma bayyana cewa hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin jihar za ta fitar da cikakkun ka’idojin aiwatar da wannan tsari nan gaba kaɗan.

Source: Facebook
Wane buri Uba Sani yake da shi?
Gwamna Uba Sani ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa wannan sabon tsari zai ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa, ya rage yawan barin aiki, tare da ɗaga matakin ilimi sosai a faɗin jihar Kaduna.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da karfafa hukumomin gwamnati da kuma zuba jari a abubuwan da za su amfani jama'a.
Uba Sani zai kafa gidauniyar Dahiru Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya je ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
A wajen ta'aziyyar, Uba Sani, ya yi alkawarin kafa wata gidauniya domin tunawa da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Ya bayyana cewa gudauniyar za ta rika gudanar da ayyukan alheri kamar wa’azin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai, abin da marigayin ya shahara da shi a rayuwarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
