An Yi Babban Rashi: Tsohon Sanata a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnatin jihar Delta ta tura sakon ta'aziyya game da mutuwar tsohon Sanata da ya yi bankwana da duniya
- Rasuwar Sanatan wanda ya wakilci Delta ta Arewa, Peter Nwaoboshi ya jefa al’ummar Anioma, Delta da Najeriya cikin alhini
- Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, yana yabawa jajircewar Nwaoboshi wajen kare muradun Anioma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Tsohon Sanatan da ya wakilci Delta ta Arewa a Majalisar Tarayya ya yi bankwana da duniya.
An tabbatar da rasuwar marigayin Sanata Peter Onyelukachukwu Nwaoboshi sai dai ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba.

Source: Original
Hakan na cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu wanda kakakin gwamnan, Sir Festus Ahon ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Gwamnan Delta ya yi ta'aziyyar tsohon Sanata
Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya nuna alhini matuƙa, yana cewa rasuwar Nwaoboshi babban rashi ne ga Delta, Anioma da Najeriya baki ɗaya.
A cikin sanarwar, Oborevwori ya ce marigayin jajirtaccen ɗan Delta ne kuma gagarumin mai kare muradun Anioma.
Gwamnan ya tuna rawar da Nwaoboshi ya taka a Majalisar Dattawa, musamman a matsayin shugaban kwamitin harkokin Niger Delta, inda ya nuna ƙwazo da jajircewa.
An yaba gudunmawar marigayi Sanata Nwaoboshi
Oborevwori ya ce tafiyar siyasar Nwaoboshi ta samo asali ne daga sadaukarwa, kishin dimokuraɗiyya da kuma shugabanci nagari a jam’iyyar PDP ta Delta.
A cewarsa, marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma, jam’iyya da ƙasa hidima, ya bar tarihi na jarumta da biyayya.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalai, al’ummar Anioma, ‘yan APC da duk masu alaka da shi, yana roƙon Allah Ya jikansa.
Sanarwar ta ce:
“A madadin gwamnatin Jihar Delta da al’ummarta, ina jimamin rasuwar abokina wanda na ke kauna, Sanata Peter Onyelukachukwu Nwaoboshi.

Kara karanta wannan
Gwamna Fubara ya fadi biliyoyin da ya tarar a asusun Rivers bayan cire dokar ta baci
"Ina mika ta’aziyyata ga iyalansa na kusa, al’ummar Anioma, mambobin jam’iyyarmu mai girma ta APC da dukkan wadanda rayuwarsa ta taba.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ji kansa da rahama, ya ba iyalansa, abokansa da makusantansa ƙarfin zuciya da juriya domin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.”
A cewar gwamnan, marigayin ɗan majalisar ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa, jam’iyyarsa da ƙasa hidima.
Sanata Nwaoboshi ya kasance mamba a Majalisar Dokoki ta Ƙasa daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Ya ce:
“Tafiyar siyasar Sanata Nwaoboshi da hawansa zuwa manyan mukamai ta ginu ne kan cikakken tarihin siyasa, hidima ba tare da son kai ba, da jajircewa wajen kare ka’idojin dimokuraɗiyya."
Mataimakin gwamnan Bayelsa ya mutu
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya tabbatar da rasuwar mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo bayan ya fito aiki.
Gwamnatin Bayelsa ta ayyana zaman makokin kwanaki uku domin jimamin wannan rashi tare da sauke tutoci a jihar mai arzikin mai.
Gwamna Diri ya aika sakon ta'aziyya ga matar Lawrence Ewhrudjakpo, 'ya'yansa da sauran 'yan uwa da al'ummar jihar Bayelsa.
Asali: Legit.ng
