Tinubu Ya Fadi Alkawarin da Ya Yi wa Amurka da Turai kan Tsaron Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da kafa 'yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro da ƙarfafa mulki a ƙasa
- Tinubu ya bayyana cewa ya ba Amurka da abokan hulɗar Najeriya a Turai tabbacin cewa Najeriya za ta aiwatar da tsarin ’yan sandan jihohi
- Shugaban ya kuma matsa lamba kan ’yancin ƙananan hukumomi tare da kira ga gwamnonin jihohi su daina riƙe kuɗinsu a yayin taron APC
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa wannan mataki ya zama wajibi domin inganta tsaron cikin gida da kuma ƙarfafa tsarin mulki a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar APC karo na 14 da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya yi magana kan manyan ƙalubalen tsaro da siyasa da ke fuskantar ƙasar.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin matsin lamba kan matsalar tsaro a faɗin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkawarin Bola Tinubu ga Amurka da Turai
Shugaba Tinubu ya shaida wa jagororin jam’iyyar cewa kwanan nan ya yi doguwar tattaunawa da abokan hulɗar Najeriya daga Amurka da Turai, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da dokar kafa ’yan sandan jihohi.
Ya ce kafa irin wannan tsari zai taimaka matuƙa wajen rage matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, tare da bai wa jihohi damar ɗaukar nauyin kare al’ummominsu yadda ya dace.
Shugaban ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar APC za ta bayar da cikakken goyon baya domin cimma wannan buri.
Vanguard ta rahoto ya ce ya bayyana wa abokan hulɗar ƙasashen waje cewa yana da jam’iyya da zai dogara da ita wajen ganin an cimma nasarar kudirin.
Maganar inganta shugabanci a Najeriya
Tinubu ya yi kira ga shugabannin APC a dukkan matakai da su nuna jagoranci na gari ta hanyar son juna da sassautawa jama'a a matakin tushe.
Ya jaddada cewa shugabanci na gaskiya yana buƙatar haƙuri da juna da kuma fahimtar ra’ayoyi mabambanta, yana mai cewa irin wannan hali ne zai kawo kwanciyar hankali da ci gaba.
Shugaban ya kuma matsa lamba kan aiwatar da ’yancin ƙananan hukumomi a aikace, yana kira ga gwamnonin jihohi da su daina riƙe kuɗin da aka ware wa shugabannin ƙananan hukumomi.

Source: Facebook
A yayin taron, shugaba Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga al’ummar jihar Bayelsa bisa rasuwar mataimakin gwamnan jihar. Ya nuna alhini tare da kira ga ’yan ƙasar su yi addu’a domin zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
'Yan Neja Delta sun yabi Bola Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata tawaga ta musamman daga yankin Neja Delta ta gana da shugaba Bola Tinubu.
Tawagar ta hada da sarkin yankin da kuma wasu manyan jami'an gwamnati da suka yaba da salon mulkin shugaban kasar.
A yayin ganawar da suka yi, jama'ar Neja Delta sun bukaci shugaba Tinubu ya sake tsayawa takara a zaben 2027 mai zuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


