"Yana Sane": Diyar Buhari Ta Fadi Halin Marigayin da 'Yan Najeriya Ba Su Sani ba

"Yana Sane": Diyar Buhari Ta Fadi Halin Marigayin da 'Yan Najeriya Ba Su Sani ba

  • Daya daga cikin 'ya'yan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi tsokaci kan wasu halayen mahaifinta
  • Halima Buhari ta bayyana cewa Buhari ya fuskanci kalubale mai yawa wajen gudanar da mulkin Najeriya
  • Ta bayyana cewa Buhari ya yi mulki yana ji a ransa cewa dukkanin matakan da ya dauka za su shafi rayuwar miliyoyin mutane

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Halima Buhari, diyar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana wasu muhimman bayanai da ba kasafai ake ji ba game da rayuwar mahaifinta ta sirri.

Halima ta ce marigayi Buhari yana sane da sukar da ake yi masa a bainar jama’a da kuma takaicin da ’yan Najeriya da dama suka ji kan gwamnatinsa.

Halima Buhari ta yi magana kan halin mahaifinta
Tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, 17 ga Disamban 2025, yayin gabatar da wani littafi da tsohon Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya wallafa, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Yar Buhari ta fadi yadda ake amfani da sa hannun marigayin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halima Buhari ta yi magana a gaban mahalarta taron da suka haɗa da tsofaffin ministoci, tsofaffin gwamnoni, sarakunan gargajiya da manyan jiga-jigan jam’iyyun siyasa.

Me Halima ta ce kan marigayi Buhari?

Ta ce mahaifinta ya fahimci cewa ’yan Najeriya da dama da suka ɗora masa babban fata, musamman kan batun tsaro da farfaɗo da tattalin arziki sun ji ya basu kunya sakamakon abin da ya yi a kan mulki.

Da take yin tsokaci kan nauyin shugabanci, ta ce Buhari sau da yawa yana fuskantar kalubalen shugabantar ƙasa mai rikitarwa kamar Najeriya, jaridar Vanguard ta dauko labarin.

"A bayan kowanne jawabi, akwai mutum, wani lokaci gajiye, wani lokaci jajirtacce, wani lokaci cike da takaici, amma kullum yana sane kwarai cewa matakan da ya dauka na shafar rayukan miliyoyin mutane.”
“Wannan mutumin shi ne mahaifinmu. Na ga wani bangare na rayuwarsa da ba a taɓa ganinsa a talabijin ba, kuma ba kasafai ake rubuta shi a jaridu ba.”

Kara karanta wannan

Labarin tsohon sakataren Buhari da ministoci da mukarraban gwamnati ke shakka

- Halima Buhari

Wane halin Buhari aka fada?

Halima ta bayyana Buhari a matsayin mutum mai kamun kai, wanda ya fi sauraro fiye da magana, kuma yana ɗaukar damuwar kasa da muhimmanci a zuciyarsa.

"Na ga mutumin da yake zaune cikin nutsuwa, yana sauraro fiye da magana. Mutumin da yake damuwa da tsaron talakawa. Mutumin da yake jin zafi a zuciya kan gibin da ke tsakanin abin da aka yi alƙawari da abin da zai yiwu a aikace."
“Ga jama’a, shi ne Shugaba Buhari. Amma a gare mu a gida, shi kawai ‘Baba’ ne.”

- Halima Buhari

Ta kara da cewa shugabanci, musamman a Najeriya, ba abu ne mai sauki ba, kuma sau da yawa yana bukatar yin sadaukarwa mai wahala.

Halima Buhari ta ce mahaifinta ya san ana sukarsa
Marigayi Muhammadu Buhari tare da diyarsa Halima Buhari Hoto: @BuhariSallau1
Source: Twitter

Buhari ya san ana sukarsa

A cewarta, tsohon shugaban kasar bai taɓa boye kansa daga suka ba, kuma bai raina ra’ayoyin masu adawa da shi ba.

"Mahaifina bai rasa sanin sukar da ake yi masa ba. Ya san cewa ’yan Najeriya da dama suna ganin ya kamata a yi abubuwa da yawa ko kuma a yi su ta wata hanya daban"

Kara karanta wannan

"A bar shi ya huta": Nasir El Rufa'i ya yi magana game da littafi kan Buhari

“Yana jin muryoyin waɗanda suka ji takaici, kamar yadda yake jin godiyar waɗanda suka ji rayuwarsu ta inganta.”

- Halima Buhari

An yi sa hannun Buhari na bogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Fatima Buhari wadda take 'ya a wajen marigayi Muhammadu Buhari, ta bayyana wasu abubuwa da ta gano.

Fatima Buhari ta bayyana cewa a lokacin mulkin mahaifinta, an yi ta kirkirar sa hannunsa a wasu takardun gwamnati.

Ta jaddada cewa wannan matsala ba ta takaita ga mulkin Buhari kadai ba, inda ta ce irin wannan lamari ya taba faruwa a gwamnatocin baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng